LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda D’Banj ya yi mana fyade, ya sa aka cafke ni – Seyitan Babalola

Bayan surutan jama’a da ce-ce-ku-ce iri-iri, Seyitan Babalola wanda ta ke zargin D’banj da laifin yi mata fyade, ta fito gaban Duniya ta fitar da cikakken jawabi game da abin da ya faru. Misis Seyitan Babalola ta bada labarin yadda Tauraron ya yi mata fyade, har ta kai ‘yan sanda sun damke ta a lokacin da ta yi yunkurin kai korafi gabansu domin a nema mata hakkinta. Buduwar ta ce Tauraron ya yi mata barazana ta bakin lauyoyinsa a lokacin da ta fallasa ta’adin da ya yi mata,


sannan kuma jami’an ‘yan sanda su ka bukaci Babalola ta yi gum da bakinta. Seyitan Babalola ta ce jami’an tsaro sun kutsa cikin dakinta da karfin da yaji da sunan ‘yan aike, su ka cafke ta, su ka rufe ta a ofishin ‘yan sanda inda ta shafe kwana biyu kafin a sake ta. Ga yadda abubuwa su ka kasance daga bakin wannan Baiwar Allah:

A ranar 30 ga watan Disamba, 2018: D’banj ya shigo cikin dakina a otel, ya yi latata da ni cikin dare. A ranar 3 ga watan Yuni, 2020: D’banj ya fito ya na sukar fyade, na kira sa na fada masa yadda ya yi mani fyade a 2018.

A ranar 5 ga watan Yuni, 2020: Na fitar da takarda daga hannun lauya na. A ranar 6 ga watan Yuni, 2020: Na tafi ofishin ‘yan sanda domin in kai kuka, amma ba a saurare ni ba. A ranar 15 ga watan Yuni, 2020: Lauyan D’banj ya maida martani ga takardun Lauyana, ya bukaci a biya sa N100m. A ranar 16 ga watan Yuni, 2020:

Wasu ‘yan sanda hudu su ka shigo dakina su ka kama ni ba tare da umarnin hukuma ba. Su ka tsare ni a ofishinsu a Ikeja. A ranar 18 ga watan Yuni, 2020: Aka raba ni da ‘yanuwana, aka tursasa ni in janye jawabina. A karshe kungiyar STER ta cece ni. Seyitan Babalola ta ce tun daga wannan lokaci D’banj ya ke yi mata barazanar cewa zai iya sayen shari’a a hannun kowa a Legas, ta kuma fito ta na rokon a kawo mata agaji.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments