LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo: Yadda aka nuno wani mutumi yana bugawa matarsa dutsin guga a gaban ‘ya’yansuJim kadan bayan kammala murnar ranar Uba ta duniya, wanda aka nuno maza da mata suna nuna soyayya da jinjina ga iyayensu, wani bidiyo marar dadin ya yadu a shafukan sadarwa, inda ya nuna wani mutumi cikin fushi yana dukan wata mata da ake da tabbacin cewa matarsa ce da dutsin guga.

A farkon bidiyon dai an nuno mutumin yana umartar matar akan tayi wani abu, inda bai ma jira ta gama sauraron umarnin da yake bata ba ya bita da duka da dutsin gugar, inda ya dinga buga mata a kai, hakan yayi sanadiyyar faduwarta a kasa.

Matar ta fadi cikin abin tausayi, inda ‘ya’yanta suka fara kuka, ita kuwa an jiyo ta ne tana ihun neman taimako.

Wani mai suna @Davidnart, wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter, ya ce: “Wannan rashin imani na mutumin nan da yawa yake. Ina fatan za a rufe shi har karshen rayuwarshi.”

Bidiyon da yana ta yawo, inda mutane da dama suka dinga tofa albarkacin bakinsu a kai.

Saboda rashin kyawun bidiyon ya sanya fitaccen mawaki dan kasar Ghana mai suna Rockstone ya roki mutumin da ya sanya ya taimaka ya goge bidiyon, duk kuwa da cewa ya sanya bidiyon ne da niyyar ya nemawa matar ‘yanci. Ga dai bidiyon a kasa:


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments