LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Allah Sarki: Yadda aka yiwa Khadija mai shekaru 5 fyade da yayi sanadiyyar mutuwar taWata yarinya mai suna Khadija dake da shekaru biyar a duniya ta hadu da ajalinta sanadiyyar fyade da wani daga cikin ahalinta yayi mata a kasar Siriliyon, inda akan hanyar su ta zuwa asibiti kuma suka hadu da hatsarin mota.

Duk da yake dai likitoci sunyi kokarin ceto rayuwar yarinyar, amma abin ya gagara, sun tabbatar da mutuwar ta nada nasaba da zubar jini mai yawa, da lalacewar gurin fitsari da bahaya da ta samu sanadiyyar fyaden da kuma buguwa da ta samu a kafadar ta a lokacin hatsarin.


Tuni dai shafukan sada zumunta suka dinga wallafa labari tare da sanya kyawawan hotunan Khadija, suna jajantawa gami da Allah wadai ga masu wannan dabi’a ta fyade.

Maganar fyaden Khadija ta dawo da maganar da wasu ke sukar ra’ayin cewa shigar banza ke jawo a yiwa mata fyade, ita Khadija dai wace irin shigar banza tayi, idan ma tayi me aka gani a jikinta na sha’awa aka yi mata fyaden?

Ga wasu daga cikin hotunan Khadija da aka dinga sanyawa a shafukan sada zumunta, inda ake nema mata adalci a wajen mahukunta:
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments