--
Cin amana: Matar aure ta yiwa mazakutar mijinta 'mugun riko' har ya fadi sumamme

Cin amana: Matar aure ta yiwa mazakutar mijinta 'mugun riko' har ya fadi sumamme



Rundunar jami'an tsaro ta NSCDC ta jihar Osun a ranar Talata ta ce ta fara bincike a kan zargin wata matar aure da ragargaza mazakutar mijinta. Kakakin rundunar, Daniel Adigun, a wata takarda da ya fitar, ya ce wata mata mai suna Omolara Seriki mai zama a Ikirun, hedkwatar karamar hukumar Ifelodun ta jihar Osun ta kai karar mijinta mai suna Raheem Seriki.

Ta zargi mijinta ta da rashin daukar dawainiyarta a matsayinsa na miji da kuma mahaifin yaranta. Adigun ya kara da cewa, a yayin da aka kira Raheem don amsa tambayoyi, an gano cewa matarsa ta saba dukansa wanda hakan yasa ya samu raunika, jaridar The Punch ta ruwaito. Takardar ta ce, "Ma'auratan sun kwashe shekaru shida da aure kuma suna da 'ya'ya biyu. Raheem ya yi korafin cewa bai taba jin dadin aurensa ba saboda tsananin rikicin da suke yi da matarsa. "Ya ce hakan ne yasa ya bar gidansa da ke Ikirun ya koma Iragbiji.

"Raheem ya ce bayan kwanaki kadan da ya bar gida, wurin karfe 10 na dare wata mata ta kawo mishi abinci amma sai bata tafi ba saboda ruwan sama da ake yi. "A yayin da take zaune, sun ji ana kwankwasa kofa sannan ya je ya bude. "Bayan da ya bude kofar, sai ya ga matarsa. A take ta hango matar da ta kawo masa abinci. Babu jimawa suka fara fada tsakanin Omolara da mijinta. “Raheem ya ce matarsa ta kama gabansa inda ta yi yunkurin tsinkeshi.

Ana haka ne ya fadi sumamme. Ya tashi ya gansa a kwance a gadon asibiti bayan ya ragargaza masa gaba. “Amma a lokacin da aka tuhumi Omolara da wannan ikirarin mijinta, ta ce ta yi kokarin kare kanta ne don mijinta ya yi yunkurin shaketa. "Matar ta ce ta fara zargin mijinta da cin amana ne amma sai ta yi kokarin tabbatar da hakan. Daga nan ne ta sameshi tare da wata mace." Ba wannan karon bane na farko da mata ke illata mazansu na aure a kan kishi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Cin amana: Matar aure ta yiwa mazakutar mijinta 'mugun riko' har ya fadi sumamme "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?