--
Tsaro: An kama wani fasto da bindigu masu yawa

Tsaro: An kama wani fasto da bindigu masu yawa



'Yan sandan jihar Delta sun tabbatar da kama wani fasto na cocin Christ Holy Church, Asaba, Mr Fidelis Nwansa da aka samu da bindigu har guda shida. Mai magana da yawun rundunar, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hira da manema labarai a ranar Alhamis a garin Asaba. Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa bayan an damke shi, faston ya yi ikirarin yana aiki tare da wata kungiyar 'yan banga ne a Anambra.

A cewar, Onovwakpoyeya, tuni rundunar ta fara cikakken bincike a kan lamarin domin gano ainihin dalilin da yasa ya mallaki bindigun. "Jami'an mu sun kama wani fasto tare da bindigu shida. 'Yan sandan sun kuma kama wani shugaban kungiyar 'yan banga mai suna Freeman. "An gano bindigun shida ne cikin wani kango da ke harabar cocin a garin Asaba.

"Bayan kama shi, faston ya yi ikirarin cewa yana aiki tare da wata kungiyar 'yan banga a Anambra kuma yana amfani da bindigun ne domin kare cocinsa. "Amma a halin yanzu mun fara gudanar da binciken kwaf kwaf domin tabbatar da gaskiya a kan ikirarin da mutumin ya yi," in ji DSP Onovwakpoyeya. A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, 'yan sandan birnin tarayya Abuja sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane,

Bello Saleh na kauyen Dobi da ke karamar hukumar Gwagwalada da aka dade ana nema ruwa a jallo. A sanarwar da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a mabuyarsa da ke kauyen Paiko Kore na karamar hukumar Gwagwalada. DSP Manzah ya ce wanda ake zargin da 'yan tawagarsa sun harbe wani Ejike Idoko mazaunin kauyen Dobi har lahira a yayin da ya yi kokarin hana su tafiya da matarsa mai juna biyu. Ya ce ana cigaba da kokarin ganin an kamo sauran 'yan tawagar na Saleh tare da kwato bindigun da ke hannunsu.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tsaro: An kama wani fasto da bindigu masu yawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?