--
Tina Akello: Matar da take yiwa gawa kwalliya ana biyanta

Tina Akello: Matar da take yiwa gawa kwalliya ana biyanta



Bayan ta girma a Budalangi, Tina Akello mai shekaru 33, tana matukar son shiga aikin soja. Bata taba tunanin za tayi aiki a kusa da gawa ba, amma komai ya canja a lokacin da aminiyarta ta mutu a shekarar 2016.

Tina wacce ta koma Mombasa a shekarar 1999, tana daya daga cikin dubunnan mutanen kasar Kenya da kasuwancinsu ya durkushe saboda cutar coronavirus da ta shafi ko ina a duniya.

Sanadiyyar annobar, iya ma’aikatan lafiya kawai aka amincewa su kusanci gawar mutane, wadanda ake gaggawar binne su da sun mutu kamar yadda sharuddan ma’aikatar lafiya ta gindaya.

Kafin annobar ta shigo, Tina ta bayyanawa Tuko.co.ke cewa tana zuwa wuraren ajiye gawa da yawa a wannan yanki nasu tayi musu kwalliya kafin a binne su.

“Ita ce babbar kawata da nake so fiye da komai, ni nayi mata kwalliya a lokacin aurenta.

“A lokacin da ta mutu ni aka sake bawa damar na gyara mata jiki kafin a binne ta. A nan ne kasuwancina ya samo asali,” ta ce.

Ta kai ga yanzu tana son aikin nata kuma tana alfahari da shi.

Sai dai kuma a yanzu matar wacce ta rabu da mijinta ta shiga wani hali na neman abinda za ta samu ta ciyar da ‘ya’yanta guda biyu.

Matar wacce take hada aikin nata da kuma gyaran gashi ta ce tunda annobar corona ta barke bata samu wanda ya kirata ayi masa aiki ba ko daya.

“Ina matukar alfahari da aikina, na fara wannan aikin a shekarar 2016. Kwanan nan na samu aiki a Nairobi, inda aka kirani naje na yiwa wasu gawarwaki guda biyu kwalliya, amma ba zai yiwu naje ni ba.

“Wannan kuma ya samo asali ne saboda dokar hana zirga-zirga da gwamnati ta saka, sanadiyyar haka yasa nayi asarar KSh 50,000 a iya wannan aiki kawai. Haka nake asarar kasuwanci yanzu,” ta ce.

Tina ta kara da cewa a lokacin da komai yake tafiya yadda ya kamata, tana samun kimanin KSh 20,000 (N72,788.80) ko KSh 30,000 (N109,183.21) a kowacce gawa guda daya, amma yanzu kusan watanni biyar ba ta samu aiki ba.

A cewarta danginta basu damu da irin aikin da take yi ba, hasali ma suna goyon bayanta ne dari bisa dari.

“Suna fatan komai zai dawo daidai. Ina yin kwalliya ga matane, idan kuma namiji ne ina bari sai an sanya masa kaya tukunna,” a cewar ta.

Tina ta karyata maganar da ake na cewa duk wanda yake aikin gawa sai ya sha giya ko kuma ya sha kwaya yake iya yi.

“Ban taba amfani da giya ba, da karfin guiwa nake shiga kullum idan zan yiwa gawa kwalliya,” ta ce.

Tina ta cigaba da cewa ba wai iya kwalliya take yiwa gawarwakin ba, hatta kaya ita take sanya musu.

Ta ce wasu lokutan ‘yan uwan gawar ne suke bata irin kayan kwalliyan da za ta yi amfani da su, inda wani lokacin kuma sai taje da kanta taga yanayin gawar kafin ta san irin kayan da za tayi amfani da su.

“Duk lokacin da ban samu aiki ba, ina zama a shagona ne na gyaran gashi,” ta ce.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tina Akello: Matar da take yiwa gawa kwalliya ana biyanta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?