--
Masu zanga-zanga sun lalata ofishin jakadancin Najeriya a Indonesia

Masu zanga-zanga sun lalata ofishin jakadancin Najeriya a Indonesia

Kusan mako guda bayan da wasu mutane suka rushe gine-gine a harabar ofishin jakadancin Najeriya a birnin Accra na kasar Ghana, wasu mutane sun maimaita makamancinsa a Indonesia. Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wasu dimbin mutane sun kai hari ofishin jakadancin Najeriya da ke Jakarta, babban birnin Indonesiya.


An tattaro cewa, mutanen da suka kai wannan hari 'yan Najeriya ne masu zanga-zangar nuna bacin ransu a kan wariyar launin fata da take hakkinsu da jami'an shige da fice na Indonesiya suke yi.

A wasu faifan bidiyo da suka yadu a yanar gizo, an jiyo masu zanga-zangar dauke da alluna suna cewa, "Babu abinda Najeriya ta ke yi. Najeriya ba ta taimaka mana. Ba mu da ofishin jakadanci. Ba za mu yarda ba."

Wasu daga cikinsu an hango suna lalata wata motar bas fara a harabar ginin ofishin jakadancin, yayin da wasu suka ragargaje kofofi da da tagogin ginin. Masu zanga-zangar sun kuma ciro tutar Najeriya da ke harabar ofishin jakadancin,

suna jan ta a kasa tare da yunkurin cinna mata wuta. Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, a cikin wasu sakonni har kashi biyu da ya wallafa a kan shafinsa na Twitter, ya yi Allah wadai da harin a ranar Alhamis, yana mai bayyana hakan a matsayin "abin kunya".

Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da kokarin gano wadanda ake zargi da aikata wannan laifi. Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da hare-hare har kashi biyu da aka kai ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin Kasar Ghana a makon jiya.

Wannan lamari ya sanya majalisar Wakilai ta ce dole ne Najeriya ta dauki mataki kan harin, domin irin wannan lamari ya fara wuce gona da iri. Da yake magana a ranar Talata, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilan, ya ce nuna diflomasiya ta hanyar kawar da kai a kan lamarin ba zai magance matsalar ba. Kalli faifan bidiyon da jaridar The Cable ta wallafa a kan shafinta na Twitter:



 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Masu zanga-zanga sun lalata ofishin jakadancin Najeriya a Indonesia "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?