LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Tashin hankali: Uwa ta daukowa diyarta ‘yan daba sun yi mata fyade

Wata mai amfani da shafukan yanar gizo a kasar Uganda, Faith Mulungi, ta bayyana yadda wata mata ta daukowa ‘yar data haifa ‘yan daba suka yi mata fyade, saboda ‘yar ta bayyana cewa mijin mahaifiyartan yana lalata da ita.

Faith Mulungi ta ce: “Wannan matar ta daukowa ‘yarta ‘yan daba suka yi mata fyade, saboda ta tona asirin cewa mijin mahaifiyarta da yake yi mata bayan dawowarta gidan da zama.”

Mulungi ta bayyana cewa budurwar da aka yiwa wannan fyade dalibar jami’a ce. Inda ta ce yanzu haka tana zaune da kakarta saboda tsaro.

Mulungi ta cigaba da cewa: ‘Ta kyaleni na wallafa labarinta a shafukan sadarwa, wannan budurwa dalibar jami’a ce ba wai wani arziki ne da iyayenta ba.

“Ta ce ta manta sau nawa yayi mata fyade, sai yanzu da wannan lamari y faru duka yabi ya tada mata hankali.

“Kimanin mutane 4 zuwa 6 ne mahaifiyar yarinyar ta dauko haya su yi mata fyaden, har yanzu ko likita ba a bari ta gani ba.”
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments