--
Gwamnonin arewa za su aika da mafarauta da 'yan banga su yaƙi 'yan bindiga

Gwamnonin arewa za su aika da mafarauta da 'yan banga su yaƙi 'yan bindiga



Gwamnonin jihohin arewa sun yanke hukuncin saka mafarauta da 'yan banga domin yakar matsalar 'yan bindiga da duk wani nau'in rashin tsaro da ke yankin. Wannan ya biyo bayan yawaitar kashe-kashe a jihohin Katsina, Zamfara da sauran jihohin yankin, jaridar Daily Trust ta wallafa. Kungiyar gwamnonin arewa, wadanda suka yi taro ta yanar gizo don sake duba yanayin tsaron yankin, sun samu shugabancin Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong.

Gwamnan ya nuna damuwarsa da yadda rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a yankin wanda ya kai ga rashin rayuka da kadarori. Gwamnonin sun yanke hukuncin kafa kwamitin da zai dinga lura da tsaron yankin wanda zai samu shugabancin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi. Kwamitin ya kunshi gwamnan jihar Zamfara da na jihar Gombe a matsayin mambobi,

Kamar yadda wata takarda da daraktan yada labarai da hulda da jama'a na gwamna Lalong, Dr Makut Simon Macham ya fitar a Jos ta bayyana, ta ce gwamnonin sun shirya yakar matsalar tsaro.

Ya kara da cewa za su saka sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da shugabannin yankunan arewa don tabbatar da cewa hannun kowa ya shiga wurin yakar rashin tsaron. A bangaren saka jama'ar yankunan, an kafa kwamitin da ya kunsa gwamnonin jihohin Adamawa, Niger da Sokoto.

"Wani hukunci da aka yanke shine na saka mafarauta, 'yan banga da kungiyoyin sa kai a yankunan domin samun bayanan sirri a kan tsaron," takardar tace. A yayin jajantawa wadanda al'amarin ya shafa, kungiyar ta yi kira ga kungiyoyi da su kwantar da hankulansu domin kungiyar da gwamnatin tarayya na iyakar kokarinta wurin shawo kan matsalar tare da bada tallafi da wadanda abun ya shafa.

Kungiyar ta yi kira ga dukkan jami'an tsaron fadin kasar nan da su tashi tsaye don kawo karshen al'amuran 'yan bindigar tare da yakar duk wani nau'in rashin tsaro. A makon da ya gabata ne kungiyoyin matasa suka yi zanga-zangar lumana a jihar Katsina sakamakon rashin tsaron da ya addabi yankin.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Gwamnonin arewa za su aika da mafarauta da 'yan banga su yaƙi 'yan bindiga "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?