LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Tashin hankali: Dalibar jami’a ta mutu a dakin saurayiWata dalibar jami’ar tarayya ta Oye Ekiti, mai shekaru 21, wacce ta ziyarci saurayinta a dakinshi dake kwalejin jihar Osun, an iske gawarta a cikin dakin nashi.

Kamar yadda VoiceAirMedia ta ruwaito sunan budurwar Faderera Oleyede.

An samu gawar budurwar a dakin saurayinta a yankin Koko dake garin Iree cikin karamar hukumar Boripe, dake jihar Osun.

Saurayin shima an bayyana sunanshi da Maliki Ayo, wanda yake dalibi ne a kwalejin jihar ta Iree.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a gabanshi, kuma ya roki a boye sunanshi, marigayiyar taje dakin saurayin tare da kawarta suka kaiwa saurayin wanda yanzu ake nema ruwa ajallo aka rasa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Opalola Yemisi ya ce tuni an kai gawar marigayiyar zuwa dakin ajiye gawa domin gabatar da gwaji.

Yemisi ya bayyana cewa kawar budurwar da suka je dakin saurayin tare mai suna Adekemi Adewumi an kamata, kuma ta tabbatar da cewa sun ci abinci tare da daddare.

Sai dai ta ce ‘yan sanda suna cigaba da bincike akan lamarin.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments