--
'Talauci zai sa mutane su fara rayuwa ƙasa da naira 500 a rana'

'Talauci zai sa mutane su fara rayuwa ƙasa da naira 500 a rana'



Shugaban Bankin Duniya David Malpass, ya bayyana korona a matsayin naƙasau ga tattalin arziƙin duniya inda ya ce tattalin arziƙin zai iya shafe shekaru 10 kafin ya farfaɗo.

Ko a watan da ya gabata, sai da shugaban ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar mutum miliyan 60 za su iya faɗawa cikin matsanancin talauci sakamakon annobar korona inda ya ce mutane za su fara rayuwa ƙasa da fam 1.55 a rana.

A wata hira da BBC a jiya a Asabar, ya bayyana cewa tsananin talauci a yanzu zai iya saka wasu su rinƙa rayuwa a ƙasa da fam ɗaya a duk rana, kimanin ƙasa da naira 500 kenan.

Awani labarin nadaban kuma Yawan mutanen da korona ta kashe ya haura 400,000

Jumullar mutanen da cutar korona ta kashe a faɗin duniya sun wuce 400,000 a halin yanzu.

Kamar yadda ƙididdigar jami'ar Johns Hopkins ta wallafa a shafinta, ta ce sama da mutum miliyan 6.9 ne suka kamu da cutar tun bayan ɓullarta a garin Wuhan da ke China.

Amurka ce kan gaba a yawan masu ɗauke da cutar da mutum 1,920,061. Sai kuma ƙasar Brazil ce ta biyu da mutum 672,846, sa'annan kuma Rasha da mutum 467,073.

Amurkar dai ce kan gaba a yawan mace-mace da mutum 109,802.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "'Talauci zai sa mutane su fara rayuwa ƙasa da naira 500 a rana'"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?