LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Biyan bashi: FG za ta rabawa wasu jihohi biyar biliyan N148
ROHOTON: LEGIT.NG

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar neman a rabawa wasu jihohi biyar fiye da biliyan N148 - Za a rabawa jihohin kudin ne a matsayin biyan bashin kudaden da suka kashe domin gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya a jihohinsu - Majalisar zartawa ta tarayya (FEC) ta yi gargadin cewa daga yanzu ba zata kara biyan wata jiha bashin kudin gyaran hayoyin tarayya ba matukar ba izinin yin hakan ta samu ba daga FG

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amice da biyan wasu jihohi biyar jimillar N148,141,987,161.25 a matsayin biyan bashin kudaden da suka kashe wajen gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya a jihohinsu. Da ya ke sanar da hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ne ya gabatar da kudirin neman biyan jihohin.

Jihohin da FEC ta amince za a biya kudin sune kamar haka; Kuros Riba, Ondo, Osun, Bayelsa da Ribas. FEC ta amice da biyan jihohin adadin kudin yayin zamanta na mako - mako da ta saba gudanarwa kowacce ranar Laraba.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya jagoaranci taron FEC da aka yi ranar Laraba da ta gabata. An gudanar da taron ne ta hanyar fasahar zamani mai amfani da yanar gizo.

Kasafin kudin ya nuna cewa jihar Kuros Riba zata samu jimillar N18,394,737,608.85, jihar Ondo N7,822,147,577.08, jihar Osun N2,468,938,876.78, jihar Bayelsa N38,040,564.40,

jihar Ribas N78,953,067,518.29. Sai dai, ministan ya bayyana cewa wannan shine karo na karshe da FG zata biya wata jiha irin wannan bashi. Ya kara da cewa daga yanzu FG ba zata biya wata jiha bashin kudin gyran hanyoyin tarayya ba matukar ba FG ce ta bata izinin yin hakan ba.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments