--
Ke duniya: An yiwa jaririya ‘yar wata 3 fyade a jihar Nasarawa

Ke duniya: An yiwa jaririya ‘yar wata 3 fyade a jihar Nasarawa



An yiwa jaririya ‘yar wata uku kacal a duniya fyade a kauyen Adogi dake jihar Nasarawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yanzu haka jaririyar na asibiti tana karbar magani a asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH), sakamakon abinda ya faru da ita.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Miamuna Adam, ta sanarwa da wakilin Daily Trust a Jos cewa lamarin ya faru da tsakar daren ranar 27 ga watan Mayu, a lokacin da suke bacci, kuma kofar dakin an barta a bude saboda zafin da ake fama dashi a yankin.

“Lamarin ya faru a ranar Laraba 27 ga watan Mayun da ya gabata, a lokacin dana tashi daga bacci na tarar cewa an dauke jaririyata da misalin karfe 3 na dare. Na duba wayata wacce kusa dani lokacin da nake bacci ita ma naga bata nan,” cewar mahaifiyar yarinyar.

Maimuna ta ce tana ganowa akwai matsala a tare da ‘yarta sai ta fara ihun neman taimako, inda mutanen yankin duka suka tashi a bacci domin taimaka mata.

Ta ce duka mutanen wannan gida nasu dama makwabtansu sun bazama cikin kauyen neman jaririyar a kafa da ababen hawa, inda aka tsinto jaririyar a cikin wani kango jini na fita daga jikinta.

“An sameta a kwance a cikin kangon an cire mata wando an ajiye a gefe. Kuma duka gabanta yana zubar da jini, inda muka yi gaggawar garzayawa da ita asibiti,” cewar Maimuna.

Tayi kira ga jami’an tsaro da manyan masu fada aji a jihar ta Nasarawa da su tabbatar an kama wanda ke da hannu a wannan aika-aika domin a tabbatar da hukunci a kansa.

Matar ta ce kwana daya bayan faruwar lamarin, sun kai kara ofishin ‘yan sanda dake Adogi, domin su dauki mataki, amma babu wani abu da ya faru har yanzu.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce “ba a kawo karar wannan lamari ga ‘yan sanda ba. Na kira ofishin mu na Adogi; sun ce ba a kai musu kara ba, amma har yanzu muna cigaba da bincike akan lamarin.”



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Ke duniya: An yiwa jaririya ‘yar wata 3 fyade a jihar Nasarawa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?