--
Matsalar tsaro: Ya kamata Buhari ya san cewa hakurin ‘yan arewa ya kare, komai na iya faruwa yanzu – Dattawan Arewa

Matsalar tsaro: Ya kamata Buhari ya san cewa hakurin ‘yan arewa ya kare, komai na iya faruwa yanzu – Dattawan Arewa



 A ranar Lahadi ne kungiyar dattawan arewa (NEF) ta ce karuwar rashin tsaro da ake samu a yankin arewa babbar shaida ce dake nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin arewacin kasar sun kasa tabuka komai wajen kare rayukan al’umma, duk kuwa da rantsuwa da suka yi na daukar wannan nauyi.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi, ta bayyana cewa karuwar hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda na nuna cewa mutanen arewa an bar su a hannun ‘yan bindiga da suke yawo gari-gari suna yin abinda suke so ba tare da an dauki wani mataki ba.

Sanarwar ta ce: “Lamarin na kara ta’azzara a kowacce rana gaskiya.

“Yan bindigar da masu tada zaune tsaye sun gano matsala a fagen siyasa, inda suke amfani da ita wajen kai hare-hare kan al’umma babu gaira babu dalili.

“Ba wai muna zuzutawa bane idan muka ce mutanen arewa basu taba ganin irin wannan tashin hankali ba na kashe-kashe, fyade, garkuwa da mutane, kone kauyuka, satar shanu da sauransu, yayin da shi kuma shugaban kasa yake fitar da maganganu da alkawura wadanda basu da tasiri.

“Yanayin da mutanen jihohin Kogi zuwa Borno, Sokoto zuwa Taraba suke ciki ba abinda za a tsaya a cigaba da kallo bane.

“A matsayinmu na kungiya, mun goyi bayan miliyoyin mutane wajen yin addu’o’i da bayar da shawarwari tare da karfafa guiwa ga dukkan hukumomin dake da hakki akan kare al’ummomi.

Kungiyar tayi gargadin cewa yanzu lokaci yayi da mutane zasu tashi tsaye, inda ta kara da cewa “an san mutanen mu da hakuri da bin doka, amma ya kamata gwamnati ta sani cewa an kai ‘yan arewa makura, komai na iya faruwa.“

Kungiyar ta tunatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa samar da tsaro da kuma kyautata rayukan al’umma sune kawai abubuwan da kundin tsarin mulki ya shimfida, kuma dole dukkanin shugabanni su cika shi.

“Halin da muke ciki a yanzu ya nuna cewa gwamnatin Buhari ta gaza tabuka komai. Wannan ba mai yiwuwa bane, muna bukatar a inganta tsaro cikin gaggawa a yankin arewa.

“Mun gaji da uzuri da barazana wadanda ‘yan ta’adda suke yi mana dariya a kai, inda kuma ‘yan kasa suke ganin cewa tabbas wannan gazawa ce ta shugabanni,” cewar kungiyar.

Da take mayar da martani, fadar shugaban kasa ta shaidawa Angon Abdullahi cewa yana jagorantar kungiyar dattawan arewa wacce ke cike da fushi da rashin jituwa.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Matsalar tsaro: Ya kamata Buhari ya san cewa hakurin ‘yan arewa ya kare, komai na iya faruwa yanzu – Dattawan Arewa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?