LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gwamna El-Rufai zai sa hannu a dokar rataye masu yin fyade a Jihar KadunaA daidai lokacin da jama’a su ke kira da babbar murya ga gwamnatoci da su kawo karshen matsalar fyaden mata da kananan yara, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana inda ta sa gaba. Mai girma gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana cewa sai inda karfinsa ya kare wajen ganin doka ta yi aiki a kan duk wadanda aka kama su na aikata wannan barna a cikin jiharsa.

Kwamishinar harkokin mata ta Kaduna, Hafsat Mohammed Baba ta bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufai zai rattaba hannu a kan dokar kashe masu laifin fyade a jihar Kaduna. An rahoto gwamna Nasir El-Rufai ya na cewa: “Duk yadda na gaji ko kuma na yi laushi, zan rattaba hannu a kan dokar kashe masu fyade.”

Malam Nasir El-Rufai ya kara da cewa: “Masu fyade ba su cancanta su zauna a cikinmu a Jihar Kaduna ba." Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta ce da gaske ta ke yi wajen kawo karshen matsalar fyade da ake samu. Gwamnati ta kuma yi kira ga mabiya su bada goyon bayansu a yakin.


Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta bayyana wannan matsaya na gwamnan Kaduna ne a shafinta na Twitter. Jama’a sun fito su na tofa albarkacin bakinsu game da wannan lamari, inda wasu su ka nuna goyon bayansu ga gwamnatin, yayin da wasu kuma su ke ganin akwai gyara a matakin. Omiachi J. ya ji dadin wannan labari, ya ce gwamnatin Kadun za ta bar tarihi.

A cewarsa, babu dalilin a cigaba da kyale wanda ya yi wa mutane fyade ya na yawo acikin al’umma. Shi kuma wani Mutumi mai suna Abu Musaddiq ya bukaci gwamnati ta nuna fushinta wurin sauran miyagun da su ke garkuwa da mutane da hallaka jama’a dare da rana a Kaduna. Mubarak Zarewa ya yi kira ga gwamnan ya tunbubi masana shari’a tukuna. Shi kuma wani ya ce kisa ba zai kawo karshen matslar ba, ya gargadi gwamnan ya sake tunani.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments