--
Hotuna: Dan majalisa ya rabawa mutanen mazabarshi sabuwar igiya ta daure akuyoyi

Hotuna: Dan majalisa ya rabawa mutanen mazabarshi sabuwar igiya ta daure akuyoyi



Wani dan siyasa na jihar Benuwe kuma tsohon dan majalisar jiha, Hon Daniel Ukpera ya zamo abin magana a shafukan sadarwa bayan ya rabawa mutanen mazabar shi igiyar da za su dinga daure dabbobi.

A rahoton da muka samu wanda yake ta yawo a shafukan sadarwa, dan siyasar ya bayar da wadannan igiyoyi ne a matsayin nuna goyon baya wajen dokar hana kiwo a jihar.

Idan ba a manta ba a shekarun baya, jihar ta Benue ta sha fama da rikicin makiyaya da manoma, wannan rikici ya tlasta gwamnatin jihar sanya dokar hana yin kiwo a jihar.




Hon Daniel Ukpera wanda ya fito takarar dan majalisa a mazabar Guma a shekarar 2019, a karkashin jam’iyyar LP, ya yanke shawarar goyon bayan gwamnatin jihar ta hanyar raba igiyoyin.

Don nuna goyon bayansa, Ukpera ya raba wadannan igiyoyi masu ban sha’awa ga masu kiwon akuyoyi a wasu kauyuka dake karamar hukumar Makurdi a jihar domin rage yawon dabbobin, da kuma bin dokar hana kiwo a jihar.

Da yake raba igiyoyin a Imande Akpu da Tse-Chagu a ranar 9 ga watan Yuni, Hon. Ukpera ya ce yana goyon bayan gwamnatin jihar akan hana kiwo da tayi, amma yace don tabbatar da cewa mutane sun bi doka ya kamata a nuna musu yadda lamarin yake.




Ya ce ya zabi kauyukan Tse-Chagu da Imande Akpu saboda sune suka fi ko ina kiwon akuyoyi a karamar hukumar.

Da yake magana da bakin wadanda suka samu igiyoyin a Imande Akpu, John Tyeku ya nuna farin cikinsa akan abinda Hon Ukpera yayi, inda ya ce wannan abu da ya kawo musu abu ne mai kyau. Ya ce daure akuyoyi babban kalubale ne a garesu.

Tyeku ya ce: “Aladun mu koda yaushe suna nan a tsare, amma daure akuyoyi shine babban kalubalen da muke fuskanta, Allah zai taimakeka Ukpera, akan nuna kulawarka akan mutanenka.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Hotuna: Dan majalisa ya rabawa mutanen mazabarshi sabuwar igiya ta daure akuyoyi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?