LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda babbar kawata ta kashe kanta akan na kwace mata saurayi – Fa’izaWata budurwa ta kashe kanta kwanaki kadan bayan ta rasa saurayin da take matukar so fiye da komai.

Marigayiyar wacce ba a bayyana sunanta ba ta kashe kanta ne sanadiyyar kwace mata saurayi da babbar aminiyarta tayi wacce suka shafe shekaru 15 suna kawance.

Wata budurwa mai amfani da shafin sadarwa n Twitter mai suna Fa’izah, ita ce ta wallafa wannan labari, inda ta ce ta gano babbar kawartan ta kashe kanta akan wannan saurayi da duka suke matukar kauna, amma ya nuna yafi sonta akan kawartan da ta kashe kanta.

Fa’iza ta ce:

“Mun shafe shekaru 15 ina kawance da wannan yarinyar, ita ce ma babbar aminiyata, amma abin takaici mun fada soyayyar wani saurayi duka ni da ita, kuma wannan saurayin yafi sona fiye da ita.

“Saboda tsananin soyayyar da muke yi masa ta sanya muka yi fada har muka daina magana na tsawon mako biyu, sai yau nake jin labarin ta kashe kanta.“


Fa’izah ta wallafa wannan labari ne a ranar 12 ga watan Yunin nan, inda yanzu kwana biyu kenan da rasuwar kawartan, wannan lamari dai ya jawo kace-nace matuka a shafin na Fa’izah, inda mutane suka dinga sharhi, kowa na fadar albarkacin bakinsa.

To dama dai ance kishin kumallon mata, kuma kowa ya san babu abinda mata baza su iya aikatawa ba akan saurayi ko miji.

A daya bangaren kuma mun kao muku labarin yadda wata mata ‘yar kasar Indonesia ta taimakawa mijinta ya auro sabuwar mata a lokacin da take dauke da tsohon ciki.

Matar ta taimaka masa ne ganin cewa bata da karfin da za ta dinga kula da mijin nata saboda wannan ciki da take dauke da shi, hakan ya sanya ta nemowa kanta kishiya.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments