--
Gwamnatin Kano ta bude Kasuwanni tare da gindaya wasu Shariɗai

Gwamnatin Kano ta bude Kasuwanni tare da gindaya wasu Shariɗai



Kwamishinan yada labarai na Jahar kano Kano Malam. Muhammad Garba shine ya bayyana hakan.

A cikin bin umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da dokar kulle da aka yi don dakile yaduwar cutar kwayar Korona. Gwamnatin jihar Kano ta fitar da ka'idoji kan yadda jama'a zasuyi game da damar zuwa kasuwanni da wuraren ayyukan tattalin arziki don gujewa hadarin ya duwar cutar acikin Jama'a.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya ce, a cikin wata sanarwa cewa bayan tattaunawa da manyan kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da yin bita kan halin da ake ciki a Kano, yanzu haka an ba da izinin bude kasuwanni, wuraren ibada da Zirga-Zirgar mutane a ranakun Lahadi, Laraba da Juma’a daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

Ya ce gwamna Ganduje ya kira taron gaggawa tare da shugabannin kasuwa kan yadda za a tabbatar da tsaurara matakan tsaro da ka’idojin kariya a kasuwanni da wuraren kasuwanci.

Bayanin ya kara jaddada cewa ya zama wajibi ga irin wadannan wuraren don tabbatar da bin ka’idojin kare Kai wadanda suka hada da tilasta yin amfani da takunkumin fuska; samar da wuraren wankin hannu / tsaftace hannu; da kuma yawan gwada zafin jiki mai yawa akai-akai.

Kwamishinan ya yi nuni da cewa yayin da aka ɗaga waɗannan hane-hane. Zirga-Zirga tsakanin Jahohi, dokar tana nan, sai dai ban da hana shigo da kayayyakin amfani da kuma kayayakin aikin gona.

Ya ce yayin da makarantu za su kasance a rufe, sanarwar ta bukaci daliban da su yi amfani da kansu da damar rediyo da darussan talabijin da gwamnatin jihar ke daukar nauyinsu.

Kwamishinan ya kara yin bayanin cewa gwamna Ganduje ya danganta nasarar da aka samu yayin da ake rage yawan masu kamuwa da cutar ne a matakan da gwamnati da hukumomin kiwon lafiya ke dauka tare da bayar da muhimmanci ga yin addua da ulama da sauran mutanen jihar. Kuma yayi kira da a yawaita irin wadannan addu'o'in har cutar ta shafe gaba daya.

Malam Garba ya kuma yabawa jama’ar jihar saboda hakurinsu da fahimtarsu a yayin da dokar ta hana yin aiki.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Gwamnatin Kano ta bude Kasuwanni tare da gindaya wasu Shariɗai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?