LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Zanga-zanga a Minneapolis: Trump ya ɓuya a ƙarƙashin ƙasaROHOTON: BBC  HAUSA

Ta fito fili cewa sai da aka kai Shugaba Trump ɗakin ɓuya na gaggawa a Fadar White House ranar Juma'a saboda damuwar da aka shiga ta yiwuwar fuskantar barazana daga masu zanga-zanga a wajen gini.

Ana zanga-zangar ne kan kisan da wasu 'yan sanda farar-fata suka yi wa wani bakar-fata George Floyd makon jiya.

Trump dai ya shafe tsawon sa'a guda a maɓoyar, yayin da masu aiko da rahotanni ke cewa lamarin ya ƙara fargabar da hukumomi ke da ita kan wannan zanga-zanga.

Tuni dai shugaban ya fitar da jerin saƙwannin Twitter ga abokan adawarsa, inda yake ɗora alhakin tarzomar kan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ra'ayin zaman kara zube.

Sai dai wasu 'yan jam'iyyarsa ta Republican sun bayyana damuwar cewa fito-na-fiton da yake yi, mai yiwuwa na rura wutar hargitsin.

A karshen mako, 'yan sanda a kasar ta Amurka sun gwabza da masu zanga-zanga a faɗin ƙasar, yayin da aka shiga kwana na shiga na tarzoma kan kisan George Floyd.

An yi fito-na-fito
An yi fito-na-fito a gomman birane ciki har da New York da Chicago da Atlanta da Philadelphia da kuma Los Angeles.

'Yan sanda a kusa da fadar White House da ke Washington sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zangar da ke cinna wuta kan gine-gine ciki har da wata coci mai tsohon tarihi da ake kira mujami'ar shugabannin ƙasar.

Birane kusan arba'in ne suka ayyana dokar hana fita, sai dai akasari masu zanga-zanga sun yi biris.

Birane fiye da 75 ne zanga-zangar ta fantsama cikinsu, titunansu da ƙafa ta ɗauke 'yan kwanakin baya saboda cutar korona, yanzu sun cika maƙil da masu zanga-zangar riƙe da juna kafaɗa da kafaɗa suna maci.

A Minneapolis inda 'yan sanda suka kashe George Floyd, an kama wani mai babbar mota da ya tuƙa abin hawansa a guje kan cincirindon masu zanga-zanga da suka mamaye wani babban titi.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.comKARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments