--
Fyade: 'Yan sanda sun kama matashin da ya sumbaci ƙanwarsa

Fyade: 'Yan sanda sun kama matashin da ya sumbaci ƙanwarsa



Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce ta kama wani matashi ɗan shekara 23 da aka gan shi cikin wani bidiyo yana sumbatar wata ƙaramar yarinya 'yar shekara uku.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar na cewa tuni aka damƙa matashin wanda ta bayyana sunansa da Adeyeye Oluwatosin Babatunde hannun jami'an binciken manyan laifuka don gurfanar da shi a gaban kotu.

Ta ce an ja hankalinta ne kan bidiyon wanda ya baza gari ƙunshe da Adeyeye da ke garin Shagamu cikin jihar Ogun yana sumbatar 'yar kishiyar babarsa mai shekara uku.

'Yan sanda ba su bayyana laifin da suke tuhumarsa da aikatawa ba, amma sun buƙaci jama'a su ci gaba da fitowa suna magana kan cin zarafin mata da aikata lalata.

Sai dai a wani sabon bidiyo da Adeyeye ya fitar, an ga matashin yana cewa ya yi bidiyon farko ne tare da ƙanwarsa a gidansu kuma ba tare da wata muguwar niyya ba.

Sanarwar ta ce "muna godewa 'yan Najeriya waɗanda suka taimaka wajen sanar da 'yan sanda kan wannan batu. A tare, za mu iya dakatar da ayyukan fyaɗe da tozarta ƙananan yara da kuma laifukan da ake aikatawa mata da yaranmu".

Lamarin dai na faruwa daidai lokacin da aka gudanar da zanga-zanga a wasu biranen ƙasar ciki har da Legas da kuma Abuja, don matsa wa hukumomi lamba kan su ɗauki ƙwaƙƙwaran hukunci ga masu aikata fyaɗe a ƙasar.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan sanda ke cewa suna yin bakin iya kokarinsu don gano duk wanda ke da hannu a kisan wata ɗaliba ƴar jami'a da aka yi zargin yi wa fyade da kuma yi mata dukan tsiya a jihar Edo.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta aika da ƙarin ƙwararru zuwa Edo don ci gaba da bincike kan sanadin mutuwar Vera Uwaila.

Mutuwar matashiyar ta yi matuƙar tayar da hankula a ƙasar tare da sake bijiro da zazzafar muhawara game da laifukan cin zarafin mata da hukuncin da ake yanke wa masu aikata su a Najeriya.

Bayanai sun ce an yi wa ɗalibar da ke nazarin ilimin ƙananan halittu fyaɗe ne bayan ta je cocin Redeemed don yin karatu kamar yadda ta saba yi, amma sai aka je aka same ta yashe a ƙasa jina-jina.

Babu jimawa kuma sai aka samu labarin wata yarinya 'yar shekara 12 da ta shaida wa 'yan sanda a jihar Jigawa cewa ta shafe tsawon wata biyu tana fuskantar fyade daga gungun mutum 12.


Rundunar 'yan sandan Jigawa ta faɗa wa BBC cewa ta samu ƙorafin cewa wani mutum mai shekara 57 ya yi ta hilatar yarinyar zuwa wani keɓaɓɓen wuri don yin lalata da ita.

Yarinyar wadda ba a bayyana sunanta ba don kare mutuncinta ta faɗa wa 'yan sanda cewa baya ga mutumin, akwai ƙarin wasu mazan 11 da suka riƙa yi mata fyaɗe a tsawon wannan lokaci.

Tuni rundunar 'yan sandan ta kama wasu mutum 12 da ake zargi.

Shi dai, matashin da 'yan sandan Legas suka kama kan sumbatar ƙanwarsa ya ce ya yi nadama don bai san lamarin zai kai ga haka ba.

A cewarsa ya yi bidiyon ne lokacin da yake wasa da ƙanwarsa kuma a kan idon mahaifinsu tare da wani maƙwabcinsu.

Ya ce bayan ya sanya bidiyon ne a kan fuskar shafinsa na Whatsapp ne sai wata mata da ta gani ta yi zargin cewa shi mai fyaɗe ne.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Fyade: 'Yan sanda sun kama matashin da ya sumbaci ƙanwarsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?