--
Facebook: Trump ya saka Facebook cikin tsaka mai wuya

Facebook: Trump ya saka Facebook cikin tsaka mai wuya

Wannan ya kasance makon da kamfanonin fasaha da yawa suka nuna damuwarsu kan yadda za su fuskanci al'amuran bambancin launin fata da na siyasa.

A wannan makon, wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin Facebook sun bijire wa manufofin kamfanin.

Kamfanin Twitter kuwa ya auka wani yakin cacar baki da Shugaba Trump bayan da kamfanin ya gargade shi cewa wasu sakonni da ya wallafa na iya tayar da hankalin jama'a.

A halin yanzu, Mark Zuckerberg da alama zai kauce wa irin yaƙin cacar bakin, bayan da ya bayyana cewa Facebook ba zai bi irin hanyar da Twitter ya bi ba.

Amma sai ga shi yana fuskantar tawaye daga bangaren da bai zata ba.

Wasu ma'aikata sun nuna rashin gamsuwarsu a bainar jama'a, kuma matakin nasu ya tilasta wa shugabn kamfanin har sai da ya gudanar da taro tsakaninsa da dukkan bangarorin ma'aikata, inda ya yi bayanin abin takaicin da ya tilasta ma sa yanke hukunci.

Wata wasikar da Shugaban Amurka ya rubuta, wadda a ciki ya ke cewa: "Lokacin da aka tarzoma ta fara ne harbe-harba zai fara" ya janyo wannan rudani.

Babban jami'in 'yan sanda na Miami Chief Walter Headley ne ya samar da wannan kalmar a shekarar 1967, dangane da mummunan manufofin aikinsa na kiyaye ayyukan siyasa a makwabta bakar fata.

Sai dai kalaman Mark Zuckerberg a wajen taron da yayi da ama'aikatan kamfanin na Facebook sun ci karo da matsayarsa.

Bayan da aka kammala taron, an fallasa kalaman Mista Zuckerberg inda yake cewa karara, "na kyamaci" kalaman shugaban Amurka, kuma ya ce kalaman ba su dace ba halayyar shugaban Amurka na kwarai ba a irin wannan lokacin.

Lamarin ya kuma sa wasu kamfanoni kamar sun yi shelar daina shirinsu na kulla yarjjeniya ko ci gaba da iki da Facebook saboda kin daukan matakin kan Mista Trump kamar yadda Twitter yayi.

Ga sakon da Oren Frank, shugaban kamfanin Talk Space ya wallafa a Twitter yana sanar da janyewar kamfaninsa daga wani aikin hadin gwuiwa da ya shirya yi da kamfanin na Mista Zuckerberg.



 Duk lokacin da Shugaban kasa ya gabatar da wani abu mai sosa zuciya, a kan sami karin kira daga ciki da wajen kamfanin domin sauya wa Mark Zuckerberg hanya.

Amma Kara Swisher, marubuciya kan batutuwar fasahar sadarwa a Jaridar New York, ta ce da wuya manufofin Facebook su sauya duk da kalubalen cikin gida da kamfanin ke fuskanta daga ma'aikatansa.

Ko dai mutane ba sa yarda da ra'ayin Mista Zuckerberg kan kalaman Shugaba Trump, Ms Swisher ta bayar da hujjar cewa Facebook zai ci gaba da yin gaban kansa saboda karfin da yake da shi a harkar tallace-tallace irin na intanet.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Facebook: Trump ya saka Facebook cikin tsaka mai wuya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?