--
FBI ta nemi taimakon kama wasu 'yan Najeriya da suka aikata zambar $6m

FBI ta nemi taimakon kama wasu 'yan Najeriya da suka aikata zambar $6m



Gwamnatin Amurka tana bincike kan wasu 'yan Najeriya shida da suka aikata laifin zamba ta email wanda miliyoyin daloli ke gudana a cikinsa - Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka, FBI, a ranar Asabar, 27 ga watan Yuni, ta bayyana sunaye da fuskokin mutane shidan da ta ke nema ruwa a jallo


FBI ta bukaci jama'a da su taimaka wajen samar da muhimman bayanai da za su kai ga kama wadanda ake zargi Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka, FBI, ta bukaci taimakon al'umma wajen gano wasu 'yan Najeriya shida da ake zargi da hannu a cikin wata badakalar dala miliyan 6.

FBI cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Asabar 27 ga watan Yuni, ta bayyana sunaye da hotunan mutum shidan da ta ke nema ruwa a jallo.

A sakon da ta FBI ta wallafa, ta sanar da cewa mutanen da ta ke nema ruwa a jallo sun aikata wata zamba da makudan kudi da sun kai dala miliyan shida. Hukumar ta ce mutanen sun ha'inci 'yan kasuwa ta hanyar sakonnin email wajen aikata wannan mummunar badakala.


Daga cikin mutanen 10 da hukumar binciken ta kasar Amurka ke neman a taimaka mata wajen lalubo su, shida sun kasance 'yan Najeriya. Jerin mutum shidan da suka kasance 'yan kasar nan sun hadar da: Richard Izuchukwu Uzuh, Alex Afolabi Ogunshakin, Felix Osilama Okpoh, Abiola Ayorinde Kayode, Nnamdi Orson Benson da Michael Olorunyomi.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Amurka a ranar Talata, 16 ga Yuni, ta sanar da zargin da ta ke yi wa 'yan Najeriyan shida kan yin amfani da fasahar zamani wajen aikata zamba ta dala miliyan 6 (kusan Naira biliyan 3 da digo 3). Sanarwar wannan zargi ta fito ne daga bakin sakataren harkokin wajen Amurka, Michael Pompeo.

Dangane da bayanan da shafin yanar gizon ma'aikatar baitulmalin kasar ta bayyana, wadanda suka aikata laifin na zamba, 'yan tsakanin shekaru 32 zuwa 37 ne. Ana zargin mutanen shida sun yi amfani da fasahar zamani wajen yin kutse kan wasu harkokin kasuwanci na Amurka masu rauni. Mutanen shida da ake nema a yanzu sun karkatar da dukiyar wadanda abin ya shafa ta hanyar yaudara da yin amfani da wasu bayanan sirri da suka zakulo wajen yashe musu tattalin arziki.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "FBI ta nemi taimakon kama wasu 'yan Najeriya da suka aikata zambar $6m "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?