--
JAMB ta bayyana dalilin da zai sa dalibai Miliyan 1.3 ba zasu samu shiga jami’a ba a shekarar 2020

JAMB ta bayyana dalilin da zai sa dalibai Miliyan 1.3 ba zasu samu shiga jami’a ba a shekarar 2020



Akwai yiyuwar cewa dalibai Miliyan 1.3 da suka rubuta jarabawar shiga jami’a  ta JAMB ba zasu samu gurbin karatu ba a shekarar 2020.

Wannan kuwa zai farune saboda daliban sun bayyana cewa basu da sakamakon kammala Sakandire yayin rijistar JAMB.

WAEC da NECO wanda ya kamata a rubutasu a watannin Mayu da Afrilu ba’a samu Rubutawa ba saboda zuwan Annobar cutar Coronavirus/COVID-19.

JAMB ta bayyana maki 160 a matsayin wanda za’a dauki daliban jami’o’i dashi da kuma Maki 120 a matsayin wanda za’a dauki daliban kwalejojin Ilimin kimiyya dashi.

Ta kuma bayyana cewa zata fara aikin samar da Guraben karatu ga daliban da suke da sakamakon kammala Sakandire a watan Augusta me zuwa.

Rijistaran JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa sai idan dalibi ya dora sakamakon jarabawar kammala Sakandire ne kawai zasu iya samarmasa da gurbin karatu.

Ya bayyana cewa dalibai 1,889, 801 ne suka samu maki akalla 120 zuwa sama, inda yace daga ciki, 536,813 ne ke da sakamakon kammala Sakandire inda 1,352,988 basu dashi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "JAMB ta bayyana dalilin da zai sa dalibai Miliyan 1.3 ba zasu samu shiga jami’a ba a shekarar 2020"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?