--
El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda zatayi da tsagerun tiwita

El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda zatayi da tsagerun tiwita



ROHOTON: LEGIT.NG

Matar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta nemi wata shawara da ta bar mutane cike da mamaki a shafinta na twitter. Matar Nasir El-Rufai ta tambaya mabiyanta a shafinta na twitter shawara a kan ta fara rufe tsageru daga shafinta masu bibiyarta a kafar sada zumuntar ko a'a.

"In hana su ganin shafi na ta hanyar rufesu ko a'a?", wannan ce tambayar da ta yi a shafinta. Amma babban abun mamakin shine yadda Gwamna Nasir El-Rufai ya yi martani. Ya ce: "Kada ki karramasu ta hanyar rufe su kwata-kwata, ki dakatar da kanki daga ganinsu ne, ta yadda za su yi ta ihunsu ba tare da kin san suna yi ba!"
Tambayar Hadiza ta zo ne kwanaki kadan bayan da ta yi murnar samun mabiya dubu tamanin a shafinta na twitter. Hakan kuwa ta faru ne bayan da ake ta zantuka a kan kashe-kashen da ya ta'azzara a yankin kudancin Kaduna da ke arewa maso yammacin jihar. An zargi matar gwamnan da nuna halin ko in kula a kan kashe-kashen da ke aukuwa a jihar.


A wani labari na daban, Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, ya ce bai taba karbar cin hanci ko bukatar hakan ba. Ya kalubalanci duk wanda ke da wani bayani mabanbancin hakan da ya fito ya bayyana.

A ranar Litinin, Sirika ya ce wannan bayanin ya zama dole sakamakon caccakarsa da 'yan Najeriya ke yi a Twitter. Sun zargi ma'aikatar sufurin jiragen saman da bukatar cin hanci kafin su amince da tashin jiragen sama yayin barkewar annobar nan.


A yayin jawabi ga kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona a Abuja, ya ce wannan ikirarin ba gaskiya bane.

"Na karanta a shafin Twitter cewa akwai wasu kudi da muke karba kafin amincewa da tashin jiragen sama. Wannan al'amari ya nisanta daga gaskiya. Kyauta ne kuma amince wa ake yi," yace. Ministan ya shawarci 'yan kasa da su daina rayuwar tuna baya don kuwa gwamnatin Buhari ta bambanta daga ta sauran.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "El-Rufai ya shawarci matarsa a kan yadda zatayi da tsagerun tiwita"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?