--
COVID-19: Gwamnatin Katsina ta dage dokar takaita zirga-zirga

COVID-19: Gwamnatin Katsina ta dage dokar takaita zirga-zirga



ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnatin jihar Katsina ta sassauta dokar kulle a jihar tsakanin karfe 10:00 na yamma zuwa 04:00 na asuba a fadin jihar. Wannan na kunshe ne a wata takarda da sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ya sa hannu sannan ya mika wa manema labarai a ranar Talata a Katsina. "Bayan takaitar yawan masu cutar coronavirus a jihar da kuma damuwar da gwamnati tare da masu ruwa da tsaki suka nuna a kan illar kullen ga rayuwar jama'a.

"Gwamnan Aminu Masari ya dage dukkan doka da aka saka a fadin jihar tun daga ranar 2 ga watan Yunin 2020," yace. "Gwamnatin ta ja kunnen jama'a da su kiyaye dukkan dokokin kiwon lafiya da na tsaro wadanda suka hada da saka takunkumin fuska, nisantar juna da kuma wanke hannu akai-akai," yace.

Ya ce mazauna jihar su sani cewa hana shiga wata jiha ko zirga-zirga tsakanin jihohi har yau yana nan. Takaita yawon babura daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe duk suna nan a jihar.

"Gwamnan Masari na rokon jama'ar jihar da su yi kokarin bin dokar sassaucin don karya ta zai sa a sake garkame jihar gabadaya," ya kara da cewa. Inuwa ya kara da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin iyakar kokarinta wajen dakile yaduwar muguwar cutar coronavirus, Premium Times ta ruwaito. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ya ruwaito cewa gwamnatin ta rufe kananan hukumomin Batagarawa da Daura sakamakon hauhawar masu cutar korona a yankin.

A wani labarin na daban, mun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, lokacin bude kasuwanni da wuraren bauta a jiharsa bai zo ba. Kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna bata aminta da bude kasuwanni da wuraren bauta ba. An rufe wadannan wuraren bautar tun a watan Maris din 2020 a matsayin hanyar dakile yaduwar mummunar annobar coronavirus a fadin jihar.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Gwamnatin Katsina ta dage dokar takaita zirga-zirga "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?