--
Bude kasuwanni da wuraren bauta: El-Rufai ya bada sanarwa

Bude kasuwanni da wuraren bauta: El-Rufai ya bada sanarwa



ROHOTON: LEGIT.NG

A jiya Litinin, 1 ga watan Yunin 2020 ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin bude kasuwanni da wuraren bauta a fadin kasar nan. Gwamnatocin wasu jihohi tuni suka bi dokar, wasu sun ki yayin da wasu har a halin yanzu basu ce komai ba game da dokar. Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa , lokacin bude kasuwanni da wuraren bauta a jiharsa bai zo ba.

Kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna bata aminta da bude kasuwanni da wuraren bauta ba. An rufe wadannan wuraren bautar tun a watan Maris din 2020 a matsayin hanyar dakile yaduwar mummunar annobar korona a jihar. Gwamnan ya kara da cewa,:

"Gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da wasu 'yan kasuwanni da kuma malaman addinai don jin ta bakinsu amma har yanzu ba ta kammala ba.

"Har sai an kammala tuntubar tare da yanke shawara, sannan za a bada sanarwa daga bakin gwamnatin." "Jihar Kaduna bata daya daga ciikin jihohi uku da gwamnatin tarayya ta garkame, don haka bata cikin wadanda ta bai wa damar bude kasuwanni da wuraren bauta a yanzu. "Jihar Kaduna tana da tsare-tsaren bude kasuwanni da wuraren bauta wadanda za ta bi kuma ta fitar da su a makon da ya gabata ga jama'ar jihar," gwamnan ya kara da cewa.





A wani labari na daban, Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, ya ce bai taba karbar cin hanci ko bukatar hakan ba. Ya kalubalanci duk wanda ke da wani bayani mabanbancin hakan da ya fito ya bayyana. A ranar Litinin, Sirika ya ce wannan bayanin ya zama dole sakamakon caccakarsa da 'yan Najeriya ke yi a Twitter.

Sun zargi ma'aikatar sufurin jiragen saman da bukatar cin hanci kafin su amince da tashin jiragen sama yayin barkewar annobar nan. A yayin jawabi ga kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona a Abuja, ya ce wannan ikirarin ba gaskiya bane.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657



0 Response to "Bude kasuwanni da wuraren bauta: El-Rufai ya bada sanarwa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?