LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo: Yadda aka nuno Kwamishinan noma na jihar Borno yana dukan mata da bulala a bainar jama’a

Abin mamaki baya karewa a duniyar nan musamman ma a Najeriya, an kama kwamishinan noma na jihar Borno a kyamara yana dukan mata da bulala a bainar jama’a.

A wani bidiyo da yake ta faman yawo a shafukan sadarwa, kwamishinan noman na jihar Borno, Bukar Talba, an nuno shi a cikin jama’a yana dukan mata yana korar su a wajen wani taro.

Duk da dai har yanzu ba a bayyana ainahin menene ya faru ba da ya sanya yake dukan su, amma Dogo M Shettima, jami’in hukumar jin dadin jama’a a jihar, ya bayyana cewa wadanda ake dukan basu daga cikin mutanen da aka ware za a bawa taimakon kayan abinci, hakan ya sanya ake dukansu.

Ya ce: “Wadannan da ake kora ba matan aure bane kuma basu daga cikin mutanen da aka bayyana cewa za a bawa tallafi. Wadanda ake yiwa bulalan ake kora ba tsofaffi bane, kuma ba zawarawa bane, sannan basu daga cikin musakai ko kuma wadanda aka ware wadannan kaya dominsu, saboda haka dole ayi musu hukunci.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments