--
Samun gawar manomi ya kawo zanga-zanga a Kaduna

Samun gawar manomi ya kawo zanga-zanga a Kaduna

ROHOTON: LEGIT.NG

Tsintar gawar manomi ce ta janyo zanga-zanga a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.Wannan al'amarin ne yasa gwamnatin jihar ta saka dokar ta-baci ta sa'o'i 24, jaridar Daily Trust ta gano. Majiya daga jami'an da kuma mazauna yankin ta sanar da cewa matasan kabilar Hausa da na Kataf ne suka yi arangama a kan gona wacce dukkan kabilun ke ikirarin nata ne.

A yayin arangamar, matasa uku sun raunata kafin dattawan yankin su shiga tsakani don gujewa irin rikicin watan Fabrairun 1992 da na Mayu da aka yi a garin Zangon Kataf. Amma kuma abinda ya kawo rikicin ranar Alhamis da ta gabata shine kisan Yusuf Musa, dan asalin Kauru amma yana zama a Zangon Kataf inda mahaifinsa yake.

Majiya daga jami'an tsaro wacce bata bari a ambaceta ba, ta ce an kashe marigayi Musa ne a gona kuma ganin gawarsa ne ya kawo zanga-zanga tsakanin garin Zango da Bakin Kogi kusa da karamar hukumar Kauru.

"Matasa rike da makamai sun rufe titin da ya fito daga Zango zuwa Bakin Kogi, ci gaban da ya kawo cunkoson ababen hawa kafin zuwa kwamishinan 'yan sanda, Umar Musa Muri da Samuel Aruwan, kwamishinan al'amuran cikin gida tare da jami'an tsaro," yace.

Ya kara da cewa, "da gaggawa jami'an suka fara tuntubar masu ruwa da tsaki tare da rokar matasan a kan su yada makamai. "A lokacin da al'amarin yayi kamari, wakilan sun hargitsa titunan da matasan suka rufe tare da raka matafiya." Kungiyar ta waskar da matafiya daga Kaduna ta Zankuwa yayin da wadanda suka taho ta Saminaka aka waskar dasu zuwa hanyar Samaru zuwa Zango.

An gano cewa, rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Safe Haven sun bayyana a wurin tare da shawo kan matsalar. A ranar Juma'a, gwamnatin jihar ta kara tsayin dokar ta-bacin a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf. Dokar ta shafi dukkan kananan hukumomi biyun na jihar. Ya ce jami'an tsaro na kokarin ganin sun shawo kan matsalar wacce ta fara daga gona.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Samun gawar manomi ya kawo zanga-zanga a Kaduna "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?