--
An kama Maigari da Fasto da suke yiwa kananan yara fyade

An kama Maigari da Fasto da suke yiwa kananan yara fyade

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama wani Maigari da Fasto da laifin yiwa kananan yara mata fyade a jihar.

Maigarin mai suna Okon Uyoe, mai shekaru 60, wanda yake sauratar kauyen Ikot Inyang, dake cikin karamar hukumar Ibesikpo Asutan, cikin jihar Akwa Ibom, an kama shi ya yiwa wata yarinya da ya siyi kosai a wajenta mai shekara 11 fyade, inda yayi mata wayo ta biyo shi daki da nufin zai bata kudinta a ciki.

A bayanin da kakakin rundunar ‘yan sandar jihar N-nudam Fredrick yayi ya ce:

“Da shigar su dakin, mutumin da ake zargin ya kama yarinyar ta karfin tsiya yayi mata fyade ba tare da amincewarta ba.

Fredrick ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 1:12 na ranar 13 ga watan Yuni.

Haka shi ma wani Fasto mai suna Victor David an kama shi da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 8 fyade, wacce iyayenta suka aiketa ta kai masa gwangwanin madara.

Kakakin rundunar ya ce:

“A ranar 1 ga watan Afrilu da misalin karfe 2 na dare, an samu kiran waya, inda jami’an ‘yan sandan SARS suka fita suka kamo wani mutumi mai suna Peter Emmanuel Ekanem, bayan karar da aka kawo na cewa ya yiwa wata fyade.

“Bayan gabatar da bincike an gano cewa mutumin ya hada baki da wasu mutane wadanda yanzu muke neman su, inda suka yiwa budurwar fyade a cikin makarantar firamare ta Ikot Akpa Ekpuk, dake karamar hukumar Ikono.

“Mutumin ya amsa laifinsa, inda aka samu karamar bindiga a wajenshi, kuma ana cigaba da bincike a kanshi.

“A ranar 28 ga watan Mayu, da misalin karfe 9 na safe, ‘yan sanda sun kama wani mai suna Henry Okon Heny mai shekaru 30 daga kauyen Mbokpueyokan, dake karamar hukumar Urue-Offong Oruko.

‘Bayan gabatar da bincike an gano mutumin ya yiwa wata budurwa mai shekaru 17 fyade, kuma yayi barazanar kasheta idan tayi kokarin guduwa ko tona masa asiri.

Duka dai za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu bayan kammala bincike a kansu.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "An kama Maigari da Fasto da suke yiwa kananan yara fyade"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?