--
Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga

Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga



Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bai wa jama'ar jiharsa tabbacin cewa manoman jihar sai sun koma gonakinsu a bana. Kamar yadda yace suna nan suna tsara yadda za a yi,


Da yardar Allah ina tabbatar wa Zamfarawa cewa wannan damunar kowa zai yi noma." A yayin tattaunawa da BBC a shafukan sada zumunta, gwamna Matawalle ya ce yana ci gaba da tattaunawa da jami'an tsaro har da kwamishinan 'yan sanda.

Ya ce wasu tubabbun 'yan ta'adda sun same shi tare da nuna matukar alhininsu a kan yadda hare-haren nan ke ci gaba. Sanannen abu ne cewa, mutanen karkara ne kadai ke iya noma a jihar Zamfara da wasu jihohin masu makwabtaka da ita sakamakon takura su da 'yan bindiga suka yi.

Matawalle ya ce: "Tubabbun 'yan bindigar da muka yi sulhu dasu sun tabbatar da cewa da kansu za su bi sauran takwarorinsu wadanda ake zargi da kai harin don su tsawatar musu a karon karshe."

A cewarsa, "Na bada damar a ba da eka 100,000 wacce kungiyar manoman auduga ta bukata don bunkasa noman auduga da rage yawan marasa aikin yi wanda babban bankin Najeriya zai tallafa wa."

Ya tabbatar da cewa Ubangiji ne ya hore wa jihar Zamfara fadin kasa da albarkar kasar noma. Amma Bello Matawalle ya ce, matukar gwamnonin yankin basu daura damarar magance rikice-rikicen da kansu ba, za ta yuwu a ci gaba da samun wannan matsalar ta tabarbarewar tsaro a yankin.


"Idan taro za a yi da irin wadannan mutane da suka ce sun yarda da sulhu, to mu gwamnonin sai mun taru gaba daya. Kuma mu tabbatar da mun aiwatar da duk matsayar da muka cimma,"


Gwamna Matawalle yace. Ya kara da cewa, babu wanda zai zo har gida ya magance wa al'ummarsu matsala face su gwamnonin da kansu. "Duk yadda muke tunanin za mu sa wani ya dauka mataki,


wallahi ba za su yi kamar yadda muke so ba. Wannan ce gaskiyar lamarin," Gwamnan yace. Bello yace, masu kai hare-haren kullum kukansu shine an mayar da su koma baya, kamar babu su gaba daya. Ba a sanya su cikin shirye-shirye da romon damokaradiyya.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?