LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yankewa Inusa Yellow hukuncin shekaru 26 a gidan yariWata babbar kotun tarayya dake zamanta a Yenagoa, babbar birnin jihar Bayelsa, ta yanke hukunci kan lamarin matashin jihar Kano da ya dauki budurwarsa daga jiharta zuwa Kano. Kotun ta zargi Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Inusa Yellow da zargin garkuwa da Ese Oruru daga gidansu a Bayelsa zuwa Kano tana yan karamar yarinya sannan ya Musluntar da ita kuma ya aure ta. Kotun karkashin jagoranicn Alkali Jane Inyang ta yankewa Yunusa Dahiru shekaru 26 a kurkuku kan laifuka biyar.

Idan baku manta ba, Saurayin Ese, Yunusa Dahiru, ya gudu da ita ne tun a ranar 12 ga watan Agustan 2015, inda ya dauke ta a shagon mahaifiyarta dake birnin Yenagoa a jihar Bayelsa. Rahotanni sun bayyana cewa a wancan lokaci, Ese ba ta wuci shekaru 13 da haihuwa ba, inda Yunusa ya tafi da ita Kano kuma ya aure ta tare da musuluntar da ita a fadar tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusu II.

A ranar 29 ga watan Fabrairu, 2016, jami'an 'yan sandan jihar Kano suka ceto Ese kuma suka danka ta a hannun kulawar gwamnatin jihar, inda bincike ya bayyana cewa tana dauke da juna biyu har na watanni biyar. A takaicen-takaicewa, Ese ta koma mahaifar iyayenta tare da jaririn ta inda take ci gaba da karatu kuma a halin yanzu ta kammala karatun sakandire. Sai dai babban abinda ke ci musu tuwo a kwarya shine yadda suka ji shiru akan alkawurran da gwamnati ta dauka, duba da biye-biye da mahaifin Ese ke yi amma tamkar an aika bawa garinsu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments