LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da duminsa: An samu karin mutum 284 dauke da korona, jihohin Legas, Rivers da Oyo ke kan gabaKamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bayyana, a yau 20 ga watan Mayun 2020, an samu karin mutum 284 dauke da cutar korona a fadin kasar nan. Jihar Legas na da mutum 199 da aka tabbatar suna dauke da cutar yayin da jihar Rivers ke biye da ita da mutum 26. Jihar Oyo na da mutum 19 da aka tabbatar suna dauke da cutar yayin da babban birnin tarayyar Najeriya,

Abuja, da jihar Borno ke da takwas-takwas. Jihar Filato da ke arewacin Najeriya na da mutum bakwai, jihar Jigawa na da mutum shida sai kuma babbar cibiyar kasuwancin arewa, wato jihar Kano na da karin mutum biyar. Jihar Abia na da mutum biyu sai jihohin Ekiti, Delta, Kwara da Taraba da ke da mutum daddaya. A yau dai jimillar masu cutar korona a fadin Najeriya ya kai 6,677. Mutum 1,840 ne suka warke garas kuma aka sallamesu daga asibiti yayin da aka rasa rayuka 200 sanadiyyar annobar da ta game duniya. KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments