--
Yawan mace-mace ya jefa masu hakar kabari cikin firgici a Kano

Yawan mace-mace ya jefa masu hakar kabari cikin firgici a Kano



Masu hakar kabari a jihar Kano sun bayyana damuwarsu matuka kan yadda likafar yawan mace-mace ke ci gaba a jihar babu sassauci. Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, masu hakar gidan na gaskiya sun ce a halin yanzu, lamarin ya kai ga har ta mafi akasarin abokanan aikinsu sun kwanta dama yayin da rayukan dumbin mutane ke ci gaba da cin karo da ajali a jihar.

Makonni kadan da suka gabata rahotanni kan yawan mace-macen mutane musamman dattawa a jihar Kano sun yadu a kafofin sadarwa gami da gudana a kan harsunan mutane a nan gida da kuma ketare. Binciken kwamitin kar ta kwana da sanya ido a kan cutar korona wanda fadar shugaban kasa ta kafa, ya nuna cewa mafi akasarin mace-macen da ke aukuwa a Kanon na alaka na da cutar wadda ta zamto ruwan daren da ya game duniya.

Yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, daya daga cikin masu hakar kabari a makabartar Kofar Mazuga da ke cikin birnin Kano, Musa Abubakar, ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki. Yana mai cewa, a tsakanin makonni biyu, biyar daga cikin abokanan aikinsa sun yi kacibus da ajali sakamakon 'yar gajeruwar rashin lafiya da har yanzu ba a tantance kowace iri ba ce.

"Bari ku ji na fada muku, annobar wannan yawan mace-mace ta yi awon gaba da abokanan aiki na biyar. Dukkansu sun mutu bayan fama da 'yar takaitacciyar rashin lafiya. Halin da ake a yanzu ya munana, sai dai Allah ya kawo mana dauki", inji shi.

Malam Musa wanda ya kai kimanin shekaru 75 a duniya, ya bayyana dimuwa kan yadda babu kakkauta wa suka binne sabbin gawawwakin mutane a 'yan kwanakin da suka gabata. Ya bayyana cewa akwai lokacin da a yini daya sun haka kaburbura 40 da 35 da 30 cikin kwanaki uku a jere.

A cewarsa, daga farkon watan Azumi na Ramadana kawo yanzu, sun binne gawawwakin fiye da mutum 300 a makabartar. Ya kara da cewa, kafin bullar annobar korona a jihar, ba su taba haka kaburbura sama da 4 a rana daya ba. "Duk da cewa binne gawawwaki a yanzu ya daina firgita ni domin kuwa na shafe sama da shekaru 60 a kan wannan aiki, sai dai babu shakka yawan wannan mace-mace abin tsoro ne."

 "Amma a halin yanzu, tsoro na yana neman ya sabunta. Wannan yawan mace-mace ta saba da yadda aka saba, a baya mu kan binne akalla mutum 4 zuwa 5 a rana daya, kuma shi ma ba koda yaushe ba."  "A bisa ga al'ada, muna binne mutum 1, 2, ko 3 a rana, amma wannan lokacin muna binne mutane 40 a cikin yini daya.

Akwai lokacin da muka haƙa kabarin mutane 35 kuma washegari muka haka 30." Na rantse da Allah, tun daga ranar da watan Azumi na Ramadan ya kama har zuwa yau, mun binne gawar sama da mutum 300 a wannan makabarta. Muna cikin wani yanayi mai muni. Abokan aiki na duka sun cikin fargaba."


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yawan mace-mace ya jefa masu hakar kabari cikin firgici a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?