--
Mai shari’a Isiaka Isola Oluwa ya kwanta dama a shekara 102

Mai shari’a Isiaka Isola Oluwa ya kwanta dama a shekara 102

ROHOTON: https://hausa.legit.ng/

Alkali Isiaka Isola Oluwa ya rasu ya na da shekaru fiye da 100 - Isiaka Oluwa ya yi karatun ilmin shari’a a Landan tun a 1950s - Cif Bode George da Musliu Obanikoro sun ce Legas ta yi rashi A ranar Asabar ne Ubangiji ya yi wa tsohon alkali Isiaka Isola Oluwa wanda ke Legas rasuwa. Marigayin ya cika ne a cikin gidansa,

kuma tuni aka bizne shi tun a ranar. Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an bizne Isiaka Isola Oluwa a makarbartar musulmai ta Atan da ke garin Yaba. Alkalin ya rasu a ranar da aka tashi da azumi na 15. Isola Oluwa mai rasuwa shi ne tsohon alkalin da ya fi kowane tsufa a jihar Legas. Tarihi ya nuna cewa an haife sa ne ranar 23 ga watan Yuni, 1918 a yankin jihar Kuros-Riba.

Iyayen marigayin mutanen Legas ne da su ka tare a kudu maso kudancin kasar. Isola Oluwa ya halarci makarantar gwamnati ta Forcados da ta St Bartholomew da ke Sapele. Bayan haka marigayin ya halarci fitacciyyar makarantar nan ta King’s College ta Legas, sannan ya yi karatun gaba da sakandare a makarantar koyon aikin gona da ke Samaru. Mai shari’a Isiaka Oluwa ya yi karatun ilmin shari’a a jami’ar Landan inda aka kira shi kuliya a 1957.

Jaridar ta ce marigayi Oluwa ya taba yin aiki a matsayin malamin jami’a. Mai rasuwan ya koyar a jami’ar Ibadan tsakanin 1949 zuwa 1950. Bayan haka marigayin ya yi aikin koyarwa da na malamin noma a makarantar aikin gona da ke garin Zariya.

A shekarar 1974 aka nada Isiaka Isola Oluwa a matsayin alkalin babban kotu. Bayan shekaru kusan goma ya na aiki a kotun tarayya Oluwa ya yi ritaya daga aiki a Yunin 1983. Daga cikin wadanda su ka aikawa iyalin marigayin da mutanen Legas ta’aziyya akwai tsohon minista sanata Musiliu Obanikoro da jigon jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mai shari’a Isiaka Isola Oluwa ya kwanta dama a shekara 102 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?