--
Dokar kulle: Fusatattun matasa sun zane alkalan kotun tafi da gidanka a Taraba

Dokar kulle: Fusatattun matasa sun zane alkalan kotun tafi da gidanka a Taraba



ROHOTON: https://hausa.legit.ng/

Fusatattun matasa sun tashi kotun tafi da gidanka da aka kafa domin hukunta direbobin da suka karya dokar kulle a jihar Taraba - Tsananin duka ya sa alkalan kotun da tsirarun jami'an tsaron da ke wurin sun gudu zuwa cikin wata gonar rake

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an shawo kan matsalar Akalan kotun tafi da gidanka da ke hukunta direbobin da suka karya dokar hana zirga-zirga a jihar Taraba sun sha dukan tsiya a hannun wasu fusatattun matasa a ranar Litinin. Fusatattun matasan sun katse aikin kotun yayin da take zamanta a yankin karamar hukumar Gassol da ke kan babbar hanyar Wukari zuwa Jalingo, sannan sun zane alkalan kotun, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Matasan, su kusan 20, sun rufe alkalan kotun guda uku da duka. Daily Trust ta ce da kyar alkalan suka samu suka gudu zuwa cikin wata gonar rake da ke kusa da wurin domin tsira daga matasan. A cewar Daily Trust, hatta tsirarun jami'an rundunar 'yan sanda da takwarorinsu na NSCDC da ke gadin kotun sai guduwa suka yi saboda ba zasu iya dakatar da fusatattun matasan ba.

Matasan sun lalata dukkan takardu da sauran kayan aikin kotun tare da yin awon gaba da 'yan kudaden da aka ci tarar direbobi. Wani shaidar gani da ido ya sanar da Daily Trust cewa, "kawai ganin fusatattun matasan mu ka yi kamar daga sama, kuma basu wani bata lokaci ba wajen fara dukan alkalan kotun."

Daily Trust ta ce bincikenta ya gano cewar yanzu haka jami'an rundunar 'yan sanda sun fara farautar matasan wadannan matasa domin gurfanar da su. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin. "An samu matsala da wasu fusatattun matasa a Tella, wadanda suka katse zaman kotun tafi da gidanka duk da yanzu an shawo kan lamarin," a cewarsa.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Dokar kulle: Fusatattun matasa sun zane alkalan kotun tafi da gidanka a Taraba "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?