--
Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666



Rohoton:https://www.bbc.com/hausa

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar.

Wannan ya biyo bayan samun ƙarin mutum 64 da aka yi a ranar Litinin.

Kazalika ta ce ƙarin wasu shida sun rasa rayukansu sakamakon cutar, abin da ya kawo jumillar adadinsu zuwa 32.

Har wa yau, ƙarin mutum 13 sun warke daga cutar kuma an sallame su - jumillar adadinsu 63.



Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar a daren Litinin ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,933.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa dokar saka takunkumi tare da kafa kotuna na musamman domin hukunta wadanda aka kama ba tare da takunkumin ba.

Jihar ta kuma tsawaita dokar kulle da mako guda nan gaba a kokarin da take na shawo kan annobar.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa.

Jihohi makwabtan Kano ma na ci gaba da fama - Katsina na da mutum 205, Jigawa na da 118, Bauchi na da 182, Kaduna na da 111.

Ya zuwa daren Litinin 11 ga watan Mayu, mutum 4,641 ne suka harbu da cutar korona a Najeriya, yayin da 150 suka rasu da kuma 902 da suka warke kuma aka sallame su.



 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?