--
Yadda bidiyon rawar matan Hausawa ya bar baya da ƙura

Yadda bidiyon rawar matan Hausawa ya bar baya da ƙura



Hausawa kan ce Sallah ta wuce ta bar wawa da bashi, amma a wannan karon sallar wucewa ta yi ta bar mutane da luguden laɓɓa kan wasu jerin bidiyo na matan aure suna rawa a gaban mazajensu a Najeriya.

A farkon wannan makon ne aka fara ganin wasu bidiyo ɗaya bayan ɗaya na yadda mace ke bayyana cikin kwalliya tana bin wata waƙa da ake rerawa mai taken "Jarumar Mata" wacce mawaƙi Hamisu Breaker ya yi.

A bidiyon dai yawanci matan kan fito ne cikin rausaya har su isa gaban mazajen nasu wadanda su kuma ke zaune suna kallonsu, yayin da wasu kuma mazan ke tashi su taya su rawar ko ma su yi musu liƙin kuɗi.

Bidiyon sun yaɗu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta inda aka yi musu take da #HusbandDanceChallenge, wato gasar yin rawa a gaban miji.

Ga alama dai an kirkiri yin hakan ne don ko dai a yi wa masu gida barka da sallah ko kuma a debe musu kewar zaman gida a lokacin kullen annobar cutar korona ta hanyar ƙirƙirar sabon abu.

Jim kaɗan da ɓullar bidiyon sai suka ja hankali sosai tare da zazzafar muhawara kan dacewa ko rashin dacewar lamarin. Shafukan Facebook da Twitter da Instagram sun dauki wuta inda aka dinga musayar ra'ayoyi tsakanin mutane kan wannan abu.

Akwai masu ganin wannan abu ba komai ba ne illa raha da kuma sauyawar zamani, sannan suna ganin an burge matuka.

Sai dai a hannu guda akwai dumbin mutane da ke jin cewa an kaucewa dokoki na addini da kyawawan al'adu na Bahaushe, don bai dace a ga matar aure tana tikar rawa har a dinga yaɗawa ba.

Suna ganin da a ce a gaban mijinta kawai ta yi ba tare da an nada a bidiyo an yaɗa ba da ya fi alkhairi.

Wasu rahotannin da ba su da tushe na cewa har auren daya daga cikin matan ya mutu sakamakon yaɗa bidiyon da ta yi ba tare da mijin ya sani ba.

Amma a iya binciken da BBC ta yi ba ta gano gaskiyar wannan labari ba har zuwa yanzu.

Daidan wani, karkataccen wani
Matasa maza da mata sun bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta kamar haka;

Ga abin da wani matashin lauya a Kano Sunusi Umar Sadiq ya wallafa a Facebook:

''Wai yaushe ma matar aure ta yi lalacewar da wai ita ce za ta yi rawa dan nishadantar da miji? Ai wannan aikin bayi ne! ''Da kuma ya zama babu bayi sai aka koma amfani da mata masu zaman kansu. Sune suke bin masu kalangu da sauran makada. Daga baya su ake debowa taron siyasa su yi 'cajin batir'.




Najwa S Ahmed ta rubutawa a Facebook cewa:

''Gaba kaɗan za a fara sirrin bayyana abin da ke faruwa a ɗakin ma'aurata kuma dakikan mata za su zo nan su ce 'yan arewa ba su iya soyayya ba. ''Ba ku san yadda kuke lalata tarbiyar yara kanana ba ne Wallahi. Kuna ta bata mana tarbiyyar kanne da yara haka kawai.''

Al-Hafiz Nafi'u Usman Rabi'u ya yi tur da Allah-wadai da wannan lamari da ya kira kauce dokokin Ubangiji, kamar haka:

 Furaira Bagel kuwa na ganin bai kamata a bata kokaci wajen yin tofin Allah-tsine ga matan ba don kuwa dukkansu sun mallaki hankalinsu kuma sun san abin da yaduwar bidiyon ka iya jawowa.

A ganinta gara a mayar da hankali kan wasu batutuwan masu muhimmanci da suka dami arewacin Najeriya maimakon ''shiga abin da bai shafi kowa da kowa kai tsaye ba.''


Furaira na ganin masu cewa an bata al'ada fada kawai suke don su ji dadi, a ganinta ai dama tuni al'adar Malam Bahaushe ta gauraye da ta wasu a bangarori daban-daban da suka hda da na biki da aure.

Nuna yatsa
Aisha Falke ita ce mai wani fitaccen shafin Instagram na Northern Hibiscus, kuma tana daya daga cikin wacce ake nunawa yatsa cewar tana assasa irin wannan lamari a tsakanin mata tare da tunzura su yin abin da bai dace ba.


Sai dai bayan da muka tuntube ta kan ko me za ta ce dangane da zargin da ake mata, sai ta ce: ''Allah Shi ne shaidata kan hakan, ba zan tsaya yin wani dogon bayani ba. Allah Yana gani kuma Yana madakata".

''Kuma wallahi ba ni ce na kirkiro wannan abu ba, a takaice ma sai da mutum uku suka fara yada nasu bidiyon sannan na gani na saka a shafina na ce matan aji su yi zan ba da naira dubu 20 ga wacce nata ya fi kyau".

''Amma da na ga an fara maganganu kan abin da na wallafa din sai na yi maza ma na cire shi.''

Ta kara da cewa: ''Lokaci fa ya yi da za a bar macen arewa ta dan dinga samun nishadi a cikin rayuwarta, wannan abin ba karamin ragewa mata damuwa zai yi ba".

''Sannan idan kin lura duk mazan nan na cikin nishadi ake abin. Sannan da ganin matan ke kin san hamshakai ne da suka san me suka taka a gidajensu ta yadda babu wani abu da zai girgiza zuciyoyinsu ko aurensu,'' in ji Falke.

Rugar tsakani
Wasu kuwa nasu ra'ayin yana tsakiya ne, sun ga laifin matan wajen yada bidiyon a shafukan sada zumunta amma kuma suna ganin ai ba kansu farau ba irin wannan abu.

Kamar dai ra'ayin Rakiya Sani Abba:



Marzouq Ungogo ma ga alama yana rugar tsakani ne wajen bayyana ra'ayi:

A idon al'ada
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza Malamin Al'ada ne a Jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto, ya kuma ce ga al'adar Bahaushe mace mallakar mijinta ce. Shi ke da hakkin sonta da sha'awarta.

''Amma ta yi rawa a kira wani ya kalla hakan bai dace ba tun gabannin zuwan Musulunci a kasar Hausa. Ko a rawar bori ai mata ba sa rawa sai sun rufe jikinsu,'' a cewar Farfesan.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yadda bidiyon rawar matan Hausawa ya bar baya da ƙura"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?