LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Minneapolis: An cinna wuta kan ofishin 'yan sanda saboda kashe baƙar-fataAn cinna wuta kan babban ofishin 'yan sanda na birnin Minneapolis a Amurka cikin dare uku na zanga-zanga kan mutuwar wani Ba'amurke ɗan asalin Afirka a hannun 'yan sanda.

Shugaba Trump ya ɗora alhakin abin da ke faruwa kan 'yan banga waɗanda ya ce suna nuna rashin mutunci ga makokin mamacin, George Floyd.

Masu zanga-zanga, haka zalika, sun fantsama tituna a sauran biranen Amurka da dama.

Masu gabatar da ƙara sun ce ba su shirya tuhumar 'yan sanda huɗu da aka ɗora wa alhakin kisan George Floyd a farkon wannan mako ba.

Babban baturen 'yan sanda na birnin a yanzu ya fito ya nemi afuwa. Sai dai ana ƙara samun kiraye-kirayen a tuhumi 'yan sandan da aikata babban laifi.

Mutuwar Mista Floyd ta janyo nuna gagarumin ɓacin ran jama'a da kuma sake bijiro da sukar da ake yi kan yadda 'yan sanda ke tunkarar Amurkawa baƙaƙen fata.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments