--
COVID-19: NCDC ta yi wa gwamnatin jihar Kogi martani

COVID-19: NCDC ta yi wa gwamnatin jihar Kogi martani


ROHOTON: LEGIT.NG

Chikwe Ihekweazu, shugaban hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC, ya yi martani bayan gwamnatin jihar Kogi ta yi watsi da alkalluman da suka nuna an samu bullar cutar korona a jihar. Sakamakon gwajin da NCDC ta fitar a daren ranar Laraba ya nuna cewa a karo na farko an samu mutum biyu da suka kamu da cutar.

Amma kwamishinan Lafiya na jihar, Saka Haruna Audu, a ranar Laraba ya musanta hakan inda ya ce jihar tana da kayan gwaji kuma ta yi gwaje gwaje masu dimbin yawa kuma duk sun nuna babu mai cutar. Kwamishinan ya ce ba za su bari matsin lamba ya saka su amincewa da sakamakon duk wani gwaji da ba Hukumar Lafiya ta jihar ta gudunar ba.

"Ba za mu amince da duk wani yunkurin tilasta mana bullar COVID-19 a jihar mu ba."

"A shirye muke mu kula da lafiyar mutanen jihar mu kuma ba mu da shawar yin siyasa da batun lafiyarsu," in ji shi. Gwamnatin ta Kogi ta ce mutane biyun da NCDC ta ce sun kamu da kwayar cutar ba yan jihar bane. Sai dai a yayin taron manema labarai na kwamitin yaki da COVID19 da ake gudanarwa kullum, Shugaban NCDC a Abuja ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin Kogi ta yi. Ya ce babu wani kokwanto ko kuskure game da adireshin mutanen da aka yi wa gwaji daga jihar Kogi.
"Ba a samu wani matsala ba game da sakamakon mutum biyun da suka kamu. Sun bi kaidojin da aka shimfida. Cibiyar Lafiya ta Tarayya ce ta tura su Asibitin Kasa. Wannan shine tsarin da ake bi idan mutum ya kamu. "Likitocin da ke Asibitin Kasa sunyi zargin COVID19 ce bisa alamomin majinyatan. Sun aike da samfurin gwaji kuma an gwada sakamako ya nuna suna dauke da kwayar cutar. Mutanen biyu mazauna Kogi ne.

"Ana laakari da inda mutum ya ke zaune ne wurin bibiyar harkar lafiya irin wannan. An bi tsarin da ya dace. Bayan sakamakon sun fito an sanar da babban likita mai sanya ido kan cututtuka masu yaduwa. "Nauyi ya rataya a kan jihar ta gano wadanda suka yi cudanya da masu cutar. Muna fatar za su yi hakan," in ji shi.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: NCDC ta yi wa gwamnatin jihar Kogi martani "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?