--
Shugaba Buhari ya cire haraji ga dukkanin kayan asibiti da za a shigar kasar

Shugaba Buhari ya cire haraji ga dukkanin kayan asibiti da za a shigar kasar

ROHOTON: https://www.bbc.com/hausa/

Gwamnatin Najeriya ta amince da cire duk wani haraji ga dukkan kayan asibiti da suka kunshi maguguna da sauran kayan aiki da za a shigar da su kasar.

Hakan kamar yadda daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Buhari kan harkar yada labarai, Tolu Ogunlesi ya wallafa a shafinsa na Twitter, bangare ne na gudunmowar kasar wajen yaki da cutar korona.

Har wa yau, shugaba Buhari ya kuma umarci hukumar Kwastan ta kasar da ka da ta tsaya bata lokaci wajen ganin irin wadannan kaya sun isa kasar.
 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Shugaba Buhari ya cire haraji ga dukkanin kayan asibiti da za a shigar kasar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?