--
Coci-19: An hana sallah a masallatai da rufe coci coci a Zamfara

Coci-19: An hana sallah a masallatai da rufe coci coci a Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe dukkanin kasuwanni da kuma hana sallah a masallatai da rufe coci coci a fadin jihar domin daƙile bazuwar cutar korona.

A jawabin da ya gabatar wa al’ummar jihar, gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun ya kuma sanar da kafa dokar hana fitar dare a faɗin jihar daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safe.

Amma a Ƙauran Namoda dokar hana fita za ta fara ne daga 6 na dare zuwa shida na safe har na tsawon mako ɗaya.

Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yawan mace-macen da aka samu a jihar.

Ya yi kira ga al’ummar Zamfara su dinga gudanar da sallah a gidajensu tun da har hakan bai saɓa wa karantarwar addinin Islama ba.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Coci-19: An hana sallah a masallatai da rufe coci coci a Zamfara"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?