\ Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Tuesday, May 5, 2020

  Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano

  Rohoton: http://hausa.legit.ng

  Gwamna Ganduje ya amince da nadin, Kabiru Inuwa, hakimin karamar hukumar Kibiya, a matsayin sabon sarkin Rano - Sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya ce Inuwa na daga cikin sunayen mutane uku da ma su nada sarki a masarautar Rano su ka aikawa gwamna Ganduje -

  Masarautr Rano ta na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamna Ganduje ya kirkira a jihar Kano Gwamnatin jihar Kano ta amince da nadin hakimin karamar hukumar Kibiya, Kabiru Inuwa, a matsayin sabon sarkin masarautar Rano.

  Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ne ya sanar da hakan da yammacin ranar Talata yayin wata ganawarsa da manema labarai a Kano.

  Alhaji ya ce Inuwa na daya daga cikin sunayen mutane uku da ma su alhakin nada sarki a masarautar su ka aikowa gwamnatin jiha. Sauran mutane biyu da aka aiko da sunayensu su ne; Muhammadu Umar; hakimin karamar hukumar Bunkure da Munir Abubakar;

  chiroman Rano. Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci sabon sarkin ya kasance mai jajircewa wajen tabbatar da adalci a tsakanin talakawansa.

  A ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, ne Allah ya yi wa tsohon sarkin Rano, Tafida Abubakar Ila (Autan bawo), rasuwa. Ya rasu ya na da shekaru 74 a duniya.

  A ranar Juma'a, 01 ga watan Mayu, aka kwantar da tsohon sarki Ila a asibitin koyarwa na Malam Aminu (AKTH) da ke birnin Kano bayan ya kamu da wata rashin lafiya da ba a bayyanata ba.

  Dag bisani an mayar da shi asibitin kwararru da ke Nasarawa a birnin Kano, inda ya mutu washegari, ranar Asabar. Masarautr Rano na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamna Ganduje ya kirkira a jihar Kano.

  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

  KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

  KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano Rating: 5 Reviewed By: Admin