--
Akwai matsin lamba ta lallai sai an samu bullar cutar korona a jihar Kogi - Bello

Akwai matsin lamba ta lallai sai an samu bullar cutar korona a jihar Kogi - Bello

Rohoton: http://hausa.legit.ng

Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya. Gwamnatin jihar ta ce wannan yana daya daga cikin makarkashiyar da ake kulla wa na neman sai an tursasawa kowace jiha a fadin Najeriya samun bullar cutar korona.


Ta yi zargin cewa "a baya-bayan nan akwai miyagun da ke ci gaba da matsin lamba ta lallai sai an lalubo masu cutar tare da kaddamar da bullar ta a jihar." A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin Kogi ta yi zargin yadda wasu masu wannan mummunar bukata ke huro wutar ayyana samun bullar cutar a jihar.

Sai dai fa gwamnati jihar ba ta fayyace ainihin masu neman kulla tuggun da zai shuka wannan mummunar badakala ba. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya yi zargin cewa,


akwai yunkurin sai lallai an shigo da wannan annoba jihar Kogi. Jihar da ke yankin Arewa ta Tsakiya, tana kewaye ne da jihohin da tuni suka samu bullar annobar ta korona.

A yanzu haka jihar tana ci gaba da fafatawa da gwamnatin tarayya dangane da yadda har kawo yanzu ta ke ikirarin bata samu bullar cutar ba. Gwamnatin jihar cikin sanarwar da ta fitar ta bayyana cewa, babu yadda za a yi ta fidda bayanan karya ko kuma ta yi kagen samun bullar cutar domin biyan bukatar wasu jami'an lafiya da bata ambaci sunansu ba,

A halin yanzu dai an samu bullar cutar korona a jihohin 34 na kasar nan ciki har da birnin tarayya Abuja.

Alkaluman hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC sun tabbatar da cewa, akwai mutum 2,802 da cutar ta harba a duk fadin Najeriya. An samu bullar cutar korona cikin dukkanin jihohin Arewa ta Tsakiya in banda jihar Kogi. Ga jerin adadin mutanen da suka kamu a jihohin yankin kamar haka: Binuwai - 2; Abuja - 297; Kwara - 16; Nasarawa - 11; Neja - 4; Filato - 3.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Akwai matsin lamba ta lallai sai an samu bullar cutar korona a jihar Kogi - Bello "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?