\ Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Wednesday, May 6, 2020

  Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda

  Rohoton: http://hausa.legit.ng


  Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fasa rundunar Yansandan Najeriya a wani mataki na yi mata garambawul don inganta aikin ta. Kamfanin dillancin labarun Najeriya,NAN, ta ruwaito majalisar ta ce haka zai kara ma rundunar karfin, zai kara ma aikin Yansanda kima da kuma taimaka wajen tsaron al’ummar kasar.

  Hakan na daga cikin shawarwarin da kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa domin ya yi nazari game kalubalen tsaro a Najeriya tare da samar da mafita daga matsalolin tsaro a kasar. A ranar 29 ga watan Janairu ne majalisar ta kafa kwamitin a karkashin jagorancin jagoran majalisar Sanata Yahaya Abdullahi daga jahar Kebbi.


  Kum tuni majalisa ta amince da rahoton kwamitin kamar yadda kakaakin majalisar, Sanata Ajibola Basiru ya bayyana. Kakaakin majalisar ya bayyana cewa kwamitin ta bayar da shawarwari da dama masu muhimmanci matuka ga majalisar, kuma majalisar ta amince dasu duka a ranar Talata. Daga cikin shawarwarin akwai;

  Majalisa ta nemi shugaban kasa ya umarci ma’aikatar kula da aikin Yansanda da babban sufetan Yansanda su raba aikin rundunar ta hanyar ma rundunar karfi a shiyyoyin kasar. Kwamitin ta nemi gwamnatin Buhari ta kafa kwamitin bada shawari game da tsaro a matakin shiyya shiyya na Najeriya don bada shawara game da matsalolin tsaron da suka addabi shiyyar.

  Ta nemi Buhari ya kafa majalisar tsaro a shiyyoyi da zai kunshi AIG na shiyyar, kwamishinonin Yansanda da kuma sauran shuwagabannin hukumomin tsaro dake shiyyar. Sauran sun hada da shugaban sarakunan gargakiyan shiyyar, kungiyoyin addinai, kungiyoyi masu zaman kansu, wakilan Sanatoci da na yan majalisu da dai sauransu.

  Sa’annan kwamitin ta nemi shugaban kasa ya umarci babban sufetan Yansanda ya kaddamar da aikin Yansandan unguwanni tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki. Majalisar ta shawarci majalisun jahohi su samar da dokokin da zasu halasta aikin Yansandan unguwanni, sa’annan gwamnoni su samar da isassun kudade ga Yansandan unguwanni.

  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

  KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

  KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda Rating: 5 Reviewed By: Admin