--
Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci

Rohoton: http://hausa.legit.ng


Wata kotu da ke zamanta a jihar Katsina a ranar Talata ya yanke wa wani mutum mai shekaru 70, Lawal Abdullahi Izala, hukuncin daurin watanni 18 a gidan gyaran hali. An kama Izala ne a makon da ta gabata a kan zarginsa da zagin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

An gurfanar da dattijon da wasu mutane biyu a gaban kuliya a kan tuhumar furta kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye da kuma rashin yi wa hukuma da a ta hanyar furta maganganu na cin mutunci

Da ya ke magana da manema labarai a ranar Talata, Izala ya ce ya yi furucin ne a cikin fushi lokacin da ya ziyarci kauyensu ya gano cewa yan bindiga sun kashe wasu yan uwansa sun kuma sace shanu 15.

A yayin zartar da hukuncin, alkalin kotun ya ce an samu Izala da laifuka biyu na assasa fitina da rashin daa ga hukuma. An yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali na laifin farko sai kuma na shekara guda na laifi na biyu. Sai dai an bawa Izala zabin biyan tara ta ₦10,000 na laifin farkon da kuma ₦20,000 na laifin na biyu. Sahara Reporters ta ruwaito cewa wasu mutane masu tausayi a jihar sun biya wa dattijon kudin tarar da aka ci shi na ₦30,000. An kuma saki dattijon ya koma gidansa.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?