--
Najeriya: ‘An yi wa budurwa fyade ta mutu a coci’

Najeriya: ‘An yi wa budurwa fyade ta mutu a coci’

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman a shafukan sada zumunta kan wata yarinya ɗaliba ƴar jami'a da ta rasu bayan zargin yi mata fyade.

Bayanai sun ce an yi wa ɗalibar mai shekara 22 da ake kira Uwavera fyade a wata coci da ke kusa da jami'ar Benin a jihar Edo.

Batun dai ya ja hankali musamman a kafofin sadarwa na Intanet inda aka ƙirƙiri maudu'in #JusticeForUwa wato tabbatar da adalci ga Uwa.

Tuni gwamnan jihar, Godwin Obseki ya umarci rundunar ƴan sandan jihar da ta gudanar da bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a al'amarin.

A ranar Laraba ne ɗalibar mai shekara 22 da ke nazarin ilimin ƙananan halittu ta je cocin Redeemed da ke kusa da jami'ar domin yin karatu kamar yadda ta saba yi, inda aka je aka same ta yashe a kasa jina-jina.

An dai ce an rotse kan Uwavera ne da tukunyar sinadarin kashe wuta bayan an yi mata fyade.

Ƴar uwar marigayiyar, Judith Omozuwa ta shaida wa BBC cewa sai bayan kwana uku ne ta cika a asibiti.

"Da misalin karfe 6 na yamma ranar Asabar an kira babata daga coci cewa mu je ba su san abin da ya faru ga 'yar uwata ba . Wata mace wadda ta samu 'yar uwar tawa ta ce ta same ta kwance cikin jini kuma an yayyaga sikyat da dan kamfanta," in ji ta.

Ta ƙara da cewa: "sun yi mata fyade, don ba ta taba sanin ɗa namiji ba. Ina matukar son ganin an samu waɗanda suka yi mata fyade domin a hukunta su."

Sai dai Judith ta ce tuni sun kai maganar gaban ƴan sandan jihar, amma jami'an tsaron sun ce a fahimtarsu Uwavera ta rasu ne sakamakon rashin jituwarta da wasu zauna gari banza da ke unguwar Ikpoba Hill inda ta ke zaune.

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya shaida wa BBC cewa tuni suka fara bincike tun bayan da labarin yarinyar ya bazu a shafukan sada zumunta.

Lamarin dai ya ja hankalin ƴan Najeriya inda wasu suka yi alla-wadai da batun musamman a shafukan sada zumunta, inda suke ta yin kiraye-kiraye ga gwamnatoci da duk masu ruwa da tsaki da a bi wa marigayya Uwavera hakkinta domin ya zama izna ga masu son kwatanta irin haka a gaba.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Najeriya: ‘An yi wa budurwa fyade ta mutu a coci’"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?