--
Rigar kowa: Wani Matashi ya mutu sa’o’i da kammala aikin NYSC a Jihar Ebonyi

Rigar kowa: Wani Matashi ya mutu sa’o’i da kammala aikin NYSC a Jihar Ebonyi



ROHOTON: LEGIT.NG

A tsakiyar makon nan ne aka yi bikin yaye wasu jeringiyar matasan da su ka kammala aikin yi wa kasa hidima watau NYSC a fadin jihohin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da ake bikin yaye matasa da su ka bautawa kasarsu, Legit.ng Hausa ta samu labarin wani Bawan Allah da ya kwanta dama sa’o’i kadan bayan da ya karbi takardar shaidarsa.

Abubakar Sadiq Hassan wanda ake kira Abba, ya rasu yayin da ya ke hanyarsa ta dawo gida cikin iyalinsa. Abubakar Hassan mutumin Zariya, ya yi aikin bautar kasarsa ne a Ebonyi.

A kan hanyar dawowa jihar Kaduna daga garin Abakalili a Kudancin Najeriya, sai Abba ya fara rashin lafiya, inda aka garzaya aka kwantar da shi a wani babban asibiti a Benuwai.

Rahotanni sun ce an kwantar da Abubakar ne a babban asibiti gwamnatin da je garin Ijadoga da ke karamar hukumar Otukpa, jihar Benuwai. A wannan gado asibiti ne kuwa ya cika.



 Wani Baffan marigayin mai suna Isa Abbas ya bayyana cewa Abba ya kasance mai basira wanda ya fita daga jami’a da shaidar mataki na biyu watau 2:1 na Digiri a bangaren fasaha.

Marigayi Abubakar Sadiq Hassan ya karanta ilmin fasahar sinadarai ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga 2014 zuwa 2018. A bara kuma ya tafi kudu domin shirin NYSC.

‘Yanuwan wannan Bawan Allah sun bukaci a sa shi a addu’ar Ubangiji ya datar da shi da aljannar Firdaus. Wasu wadanda su ka yi karatu da Abba, sun yi masa shaida ta kwarai.

Abokan karatu su kan kira Abubakar Sadiq Hassan da Abba White ko kuma "IJMB GURU" saboda bajintar da ya nuna a wajen sharan fage a makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya.

Shi kuma wani matashin da ya ke cikin sahun wadanda su ka karkare yi wa kasarsu bauta, ya ba mutane tausayi yayin da ya tafi kabarin mahaifiyarsa dauke da satifiket dinsa.




 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Rigar kowa: Wani Matashi ya mutu sa’o’i da kammala aikin NYSC a Jihar Ebonyi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?