LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Na dauka fyade zai yi mini, ban san cewa jima’i wajibi bane idan anyi aure – Cewar amaryar da ta kashe mijinta kwana 11 da aureAn kama wata budurwa ‘yar shekara 18 a duniya da laifin kashe mijinta da yaje zai kwanta da ita a jihar Bauchi, inda tace bata san cewa jima’i wajibi bane idan anyi aure, shi yasa ta kashe shi, domin tayi tunanin fyade zai yi mata.

Yarinyar mai suna Salma Hassan, wacce ke zaune a Itas-Gadau, an kai ta ofishin ‘yan sanda na Bauchi a ranar Talata 19 ga watan Mayu, da laifin kashe mijinta da wuka kwanaki 11 kacal bayan aure.

Ta bayyanawa manema labarai cewa lokacin da mijinta ya tinkare ta da niyyar zai kwanta da ita, tayi tunanin cewa abinda yake yi ba daidai bane, sai taki amincewa. Sai mijin nata ya fara dukanta ya daureta inda ya kwanta da ita ta karfin tsiya. Ta ce sai ta dauki wuka da niyyar ta tsorata shi tsautsayi yasa ta caka mishi.

Ta ce: “Mun yi aure, muna son junan mu.

“Ban taba sanin cewa jima’i wajibi bane idan anyi aure. To a cikin wannan daren ya tinkaro ni da niyyar zai kwanta dani, sai naki amincewa saboda ban taba sanin wani abu jima’i ba. Nayi tunanin. zai yi mini fyade ne.

“Sai yayi fushi, ya dinga marina da duka, yana kokarin kwanciya dani ta karfin tsiya, sai na dauki wuka domin na tsorata shi, amma sai ya cigaba da zuwa inda nake. Ban san lokacin dana caka masa wukar a kirji ba.

“Na riga na bayar da rahoton yadda lamarin ya faru, ina cikin damuwa sosai saboda ban san mai zai faru dani ba. Amma inda na san hakane da banyi abinda nayi ba.”

A cewar ‘yan sanda sun samu wuka a lokacin da suka kama Salma da laifin kisan kan.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments