--
Sassauta dokar kulle: Gwamnatin Buhari ta ba Ganduje, Bala, Zulum shawara karanta abinda tace

Sassauta dokar kulle: Gwamnatin Buhari ta ba Ganduje, Bala, Zulum shawara karanta abinda tace



Sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya yi kira ga gwamnonin jihohin da suka sassauta dokar kulle da su bi a hankali.

Mr Mustapha, yayin da yake jawabi a matsayinsa na shugaban kwamitin yaki da cutar korona na gwamnatin tarayya ranar Alhamis a Abuja, ya ce matakin sassauta dokar kullen zai iya sanya mutane su yi ta kamuwa da cutar korona.

Jihohi irin su Bauchi, Kano, Adamawa, Cross River, Borno, da kuma Ebonyi suna cikin wadanda suka sassauta dokar kullen inda suka amice a gudanar da sallolin Juma'a da na Idi.

Gabilin jihohin na ci gaba da fama da karuwar masu dauke da cutar, a daidai lokacin da suke sassautar dokar ta kulle lamarin da masana harkokin lafiya suke gani a matsayin ragon azanci.

Da ma dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da soke duk wani taron jama'a, wanda ya hada da tarukan wuraren addini, a matakin dakile yaduwar cutar ta korona.

Amma duk da haka jihohin suka dauki matakin bari a gudanar da sallolin na Juma'a da Idi.

A farkon mako, Malam Garba Shehu, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin watsa labarai ya ce abin takaici ne a ce gwamnatin tarayya tana daukar matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai daga gwamnonin jihohi.

Ya ce ''ba wai zargi muke yi ba ko kushe, amma akwai bukatar a ce ana tafiya tare saboda idan matsaya ba ta zo guda ba, da wuya a yi nasara a yaki da korona''.

Malam Garba Shehu, ya ce kwamitin da ke yaki da annobar na kasa na kokawa kan yadda matakan wasu jihohi ke warware nasarorin da ake samu akan annobar.

"Kamata ya yi kafin a dauki kowanne irin mataki, to a tuntubi masana domin neman shawarwari," in ji mai magana da yawun shugaba kasar.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Sassauta dokar kulle: Gwamnatin Buhari ta ba Ganduje, Bala, Zulum shawara karanta abinda tace"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?