--
Bidiyon wata ma'aikaciyar jinya da aka kama ta saci jinjiri

Bidiyon wata ma'aikaciyar jinya da aka kama ta saci jinjiri



Wani bidiyo ya bazu na wata ma'aikaciyar jinya da jama'a suka yi wa caa - An zargi ma'aikaciyar jinyar da yunkurin sace jariri namiji bayan haihuwarsa a asibitin - Al'amarin ya faru ne a wani asibiti da ke yankin Iweka na garin Onitsha da ke jihar Anambra Wani bidiyo mai matukar bada mamaki ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, an kama ma'aikaciyar jinya wacce ake zarginta da yunkurin satar jinjiri.

Kamar yadda rahoton ya nuna, ma'aikaciyar jinyar ta yi yunkurin satar jinjirin ne bayan haihuwarsa kuma an kama ta ne yayin da tayi nisa daga asibitin. Fusatattun jama'a ne suka zagaye ta inda suke tambayarta abinda za ta yi da sabon jinjirin. A bidiyon, ma'aikaciyar jinyar da ke sanye da kayan aiki an ganta rike da jariri rufe a cikin tsumman goyo tare da rungumesa a kirjinta.

Ma'aikaciyar jinyar ta yi ikirarin cewa za ta kai wa mahaifiyar jaririn ne shiyasa ta dauko shi. A take fusatattun mutanen da suka taru suka nuna rashin amincewarsu da labarinta don babu wanda ke amince wa a fitar da jinjiri daga asibiti. Al'amarin ya faru ne a yankin Iweka da ke Onitsha a jihar Anambra. Mediagist ta wallafa a shafin Instagram cewa:

“An zargi wata ma’aikaciyar jinya da satar jinjiri namiji bayan an kama ta dauke da yaron a yayin da tayi nisa daga asibitin. Ma'aikaciyar jinyar ta yi ikirarin cewa za ta kai wa mahaifiyar jaririn ne shiyasa ta dauko shi, amma mazauna yankin suka ce babu wanda ke amince wa a fitar da jinjiri daga asibiti.” Ga bidiyon a kasa:




 A gefe guda, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Yenagoa, babbar birnin jihar Bayelsa, ta yanke hukunci kan lamarin matashin jihar Kano da ya dauki budurwarsa daga jiharta zuwa Kano. Kotun ta zargi Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Inusa Yellow da zargin garkuwa da Ese Oruru daga gidansu a Bayelsa zuwa Kano tana yan karamar yarinya sannan ya Musluntar da ita kuma ya aure ta.

Kotun karkashin jagoranicn Alkali Jane Inyang ta yankewa Yunusa Dahiru shekaru 26 a kurkuku kan laifuka biyar. Idan baku manta ba, Saurayin Ese, Yunusa Dahiru, ya gudu da ita ne tun a ranar 12 ga watan Agustan 2015, inda ya dauke ta a shagon mahaifiyarta dake birnin Yenagoa a jihar Bayelsa. Rahotanni sun bayyana cewa a wancan lokaci, Ese ba ta wuci shekaru 13 da haihuwa ba, inda Yunusa ya tafi da ita Kano kuma ya aure ta tare da musuluntar da ita a fadar tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusu II.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Bidiyon wata ma'aikaciyar jinya da aka kama ta saci jinjiri "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?